"Ba Zan Lamunta ba," Gwamna Ya Dakatar da Mai Martaba Sarki, Ya Umarci a Kama Ƴaƴansa 2
- Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya dakatar da Sarkin Swali, Mai Martaba Wilcox Seiyefa Job sakamakon taɓarɓarewar tsaro a yankinsa
- A wata sanarwa da gwamnatin Bayelsa ta fitar, ta ce an dakatar da basaraken saboda yadda ya gaza shawo kan ayyukan kungiyoyin asiri
- Gwamnatin jihar Bayelsa ta buƙaci ƴan sanda su gaggauta kama duk mai hannu a lamarin ciki har da ƴaƴan sarkin guda biyu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Bayelsa - Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri, ya amince da dakatar da Mai Martaba Sarkin Swali da ke karamar hukumar Yenagoa, HRH Wilcox Seiyefa Job.
Gwamna Sanata Diri ya dakatar da basaraken kan zarge-zarge da dama da suka ƙunshi gaza shawo kan ayyukan ƙungiyoyin asiri a yankinsa.

Asali: Facebook
Jaridar The Nation ta tattaro cewa wannan mataki da Mai girma gwamna ya ɗauka na dakatar da sarkin zai fara aiki ne nan take.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana ganin dai matakin wani ɓangare a ƙoƙarin da gwamnatin jihar Bayelsa ke yi wajen yaki da laifuffuka da ayyukan kungiyoyin asiri a cikin al’umma.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwar hadin gwiwa da kwamishinar yada labarai, wayar da kai da dabaru, Mrs. Ebiuwou Koku-Obiyai, da kwamishinan kananan hukumomi da sarautun gargajiya, Cif Thompson Amule suka fitar.
Meyasa gwamna ya dakatar da Sarki?
Sanarwar ta bayyana cewa gwamnati ba za ta zuba ido tana kallon tsaro na tabarbarewa a cikin al’umma ba, kuma sarakuna da masu iko su ƙi ɗaukar mataki a kai.
A cewar sanarwar:
"An dakatar da Mai Martaba ne sakamakon gazawarsa wajen daukar matakin da ake tsammani a matsayinsa na sarki, musamman a yaki da ayyukan kungiyoyin asiri.
"Wasu sahihan bayanan sirri da muka samu sun nuna cewa ana zargin ‘ya’yansa biyu suna cikin masu gudanar da ayyukan asiri a Swali.”
Gwamna Diri ya umarci a kama waɗanda ake zargi
Sanarwar ta ci gaba da cewa tuni aka umarci Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar da ya ayyana wadanda ake zargi, ciki har da ‘ya’yan sarkin guda biyu, a matsayin wadanda ake nema ruwa a jallo.
Ta ce jami'an ƴan sanda za su gudanar da bincike mai zurfi kan waɗanda ake zargi, kuma da zaran sun shiga hannu, za a gurfanar da su a gaban ƙuliya.

Asali: Getty Images
Gwamnatin jihar Bayelsa ta jaddada cewa ba za ta lamunci kowane irin rashin gaskiya ko rashin daukar nauyin abubuwan da ya kamata daga sarakuna ba.
Ta ce ba za ta lamurci duk waɗannan ba musamman idan hakan zai janyo tabarbarewar tsaro da zaman lafiya, cewar rahoton The Cable.
Wannan mataki na zuwa ne a wani bangare na tsaurara matakan da gwamnatin Diri ke ɗauka a yaki da ayyukan asiri da sauran laifuka a jihar Bayelsa.
Gwamnan Bayelsa ya tuna mahaifiyarsa
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa ya tuna da mahaifiyarsa a wurin taron tunawa da ita karo na 12 da aka shirya a Ayamasa.
Sanata Diri ya ce mahaifiyarsu ta koya musu darussa na ƙauna, zaman lafiya da daraja addini, waɗanda kowa ke gani a tattare da su a yanzu.
Gwamnan ya nuna damuwa kan rasuwar mamarsa da wuri, yana mau cewa ya so a ce ta yi tsawon rai domin ta ga matakin da ƴaƴanta suka taka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng