'Yan Bindiga Sun Farmaki Manoma a Katsina, an Hallaka Bayin Allah

'Yan Bindiga Sun Farmaki Manoma a Katsina, an Hallaka Bayin Allah

  • Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari kan manoman yayin da suke ƙoƙarin share gonakinsu a jihar Katsina
  • Miyagun ƴan bindigan sun farmaki manoman ne a wasu ƙauyuka na ƙaramar hukumar Kankara ta jihar Katsina
  • Dakarun sojojin da sauran jami'an tsaro sun kai ɗaukin gaggawa bayan samun rahoton harin da ƴan bindigan suka kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Ƴan bindiga sun hallaka manoma uku a wani harin ta'addanci da suka kai a jihar Katsina.

Ƴan bindigan sun farmaki manoman ne yayin da suke share gonakinsu a ƙauyukan Azkwai Yalwa, Gidan Daudu da ke cikin ƙaramar hukumar Kankara a jihar Katsina.

'Yan bindiga sun kai hari a Katsina
'Yan bindiga sun kashe manoma a Katsina Hoto: @dikko_radda
Asali: Facebook

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun yi ɓarna a Katsina

Wata majiya ta bayyana cewa waɗanda aka kashe sun haɗa da Isah Zangon Daura, Mani Zangon Daura, da wani mutum ɗaya da ba a gano sunansa ba.

Ƴan bindigan sun kai musu harin ne a ranar Talata, 21 ga Mayun 2025 da misalin ƙarfe 5:30 na yamma.

Dakarun sojojin Najeriya da ke ƙarƙashin rundunar Operation Fansan Yanma, tare da haɗin gwiwar ƴan sanda da kuma jami’an tsaron Katsina (C-Watch), sun gaggauta zuwa wajen da lamarin ya faru, amma ƴan bindigan sun tsere kafin isowarsu.

An garzaya da waɗanda harin ya ritsa da su zuwa asibitin gwamnati, inda likitoci suka tabbatar da cewa sun mutu kafin isowarsu.

Bayan haka, an miƙa gawarwakin ga shugaban ƙauyen domin a yi musu jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Akwai matsalar rashin tsaro a jihar Katsina

Wannan mummunan hari ya sake jaddada halin rashin tsaro da ke addabar yankunan karkara a arewacin Najeriya, musamman a jihar Katsina, inda ƴan bindiga ke ci gaba da kai hare-hare kan manoma da mazauna ƙauyuka ba tare da tsoron hukuma ba.

'Yan bindiga sun yi ta'asa a Katsina
'Yan bindiga sun kashe manoma a Katsina Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Har ila yau, wannan hari ya jefa al’umma cikin firgici da fargaba, musamman a daidai lokacin da ake shirin fara aikin noma na damina.

Da dama daga cikin mazauna yankin sun nuna fargabar cewa rashin tsaro zai shafi aikin gona, wanda hakan zai iya haifar da ƙarancin abinci da tsadar rayuwa a nan gaba.

Masu ruwa da tsaki a harkar tsaro da kuma shugabannin al’umma na ci gaba da kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa domin daƙile irin wannan ta’addanci da kuma kare rayuka da dukiyoyin mutane.

Ƴan bindiga sun sace mutane a Kogi

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun yi ta'asa a wani harin ta'addanci da suka kai a jihar Kogi.

Ƴan bindigan sun yi awon gaba da mutane huɗu a wani hari da suka kai a ƙauyen Oƙoloke da ke ƙaramar hukumar Yagba ta Yamma.

Miyagun ƴan bindiga sun sake kai harin ne bayan a kwanakin baya sun yi awon gaba da basaraken ƙauyen mai shekara 90 a duniya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng