Zulum Ya Yi Karatun Ta Natsu, Ya Fadi Yadda za a Kawo Karshen Ta'addanci a Wata 6

Zulum Ya Yi Karatun Ta Natsu, Ya Fadi Yadda za a Kawo Karshen Ta'addanci a Wata 6

  • Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya taɓo batun matsalar rashin tsaron da ta addabi Arewa maso Gabas
  • Zulum ya bayyana cewa a halin da ake ciki a yanzu, ƴan ta'adda na amfani da fasahohin zamani wajen yaƙar sojojin Najeriya
  • Gwamnan Borno ya buƙaci dukkan matakan gwamnati da su haɗa kai domin ganin an kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya nuna damuwa kan taɓarɓarewar matsalar tsaro a yankin Arewa maso Gabas.

Gwamna Zulum ya bayyana cewa yanzu ƴan ta’adda suna amfani da sababbin fasahohi na zamani wajen yaƙi da sojojin Najeriya.

Zulum ya yi magana kan rashin tsaro
Zulum ya bukaci a kawo karshen ayyukan ta'addanci Hoto: @ProfZulum
Asali: Original

Zulum ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar News Central Tv a ranar Laraba, 21 ga watan Mayun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya roƙi a gaggauta ɗaukar mataki da haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da jihohi don kawo ƙarshen ta’addanci a yankin.

Zulum ya ce sojoji ba su da kayan aiki

Zulum ya bayyana cewa rundunar sojojin Najeriya ba ta da kayan aiki isassu da za su iya kai da kai da na zamani irin waɗanda ƴan ta’addan ke amfani da su.

"Sojoji ba su da kayan aikin da suka wajaba a wajen yaƙi da ƴan ta’adda, kuma ina so na bayyana muku cewa a halin yanzu, ƴan ta’adda suna amfani da fasahar zamani wajen yaƙar sojojin da ke fagen daga."

- Farfesa Babagana Umara Zulum

Ya bayyana cewa babban hafsan sojojin ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya shaida masa cewa ana buƙatar jiragen yaƙi marasa matuƙa domin inganta leƙen asiri da nasarar aiki a filin daga.

“Kwanaki kaɗan da suka gabata, na gana da hafsoshin sojojin ƙasa, ya ce yana neman jirage marasa matuƙa guda 32 don kawo ƙarshen ta’addanci, kuma yana da gaskiya."

“Kowane jirgi yana kusan Dala miliyan 5.5, to me zai hana mu haɗa ƙarfi da ƙarfe mu saya waɗannan jiragen, mu maida hankali kan matsalar tsaro?"
"Wani abu da ya kamata mu ƙara lura shi ne ya kamata sayo kayan aikin sojoji na zamani ya kasance kai tsaye daga gwamnati zuwa gwamnati domin a tabbatar da inganci."
“Idan ba haka ba, yawancin kamfanonin kwangila, ba ina cewa duka ba, idan ka ba su kuɗin, ko kayan ma ba za su saya ba."

- Farfesa Babagana Umara Zulum

Babagana Umara Zulum
Zulum ya bukaci a hada kai don magance rashin tsaro Hoto: @ProfZulum
Asali: Facebook

Zulum ya faɗi hanyar magance rashin tsaro

Sai dai Zulum ya nuna ƙwarin gwiwar cewa idan an bi hanyar da ta dace kuma dukkan matakan gwamnati suka haɗa kai, za a iya kawo ƙarshen ta’addanci cikin ƙanƙanin lokaci.

“Idan muna son mu yi abin da ya dace, za mu iya haɗa kanmu, kuma wannan haukar za ta ƙare cikin watanni shida. Amma dole sai an yi abin da ya dace.|

- Farfesa Babagana Umara Zulum

Gwamnatin Zulum ta haramta sare itace

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya rattaɓa hannu kan wasu sababbin dokoki.

A ɗaya daga cikin dokokin, Gwamna Zulum ya haramta sare itace ba bisa ƙa'ida a duk faɗin jihar Borno.

A cikin dokar an yo tanadin hukuncin ɗauri a gidan gyaran hali ko biyan tara ga duk wanda aka samu ya karya dokar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng