An Kai Karar Tinubu gaban Majalisar Dinkin Duniya kan Ta'addanci a Najeriya

An Kai Karar Tinubu gaban Majalisar Dinkin Duniya kan Ta'addanci a Najeriya

  • Ƙungiyar SERAP ta bukaci Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya yi amfani da Mataki na 99 domin kai Najeriya Kwamitin Tsaro
  • Rahoton ya nuna yadda sace-sacen mutane da kashe-kashe ke ƙaruwa a jihohin Oyo, Benue, Borno da sauran sassan Najeriya tare barazana ga fararen hula
  • SERAP ta nemi Majalisar ta sa ido kan Najeriya ta gudanar da bincike kare fararen hula da tabbatar da hukunta masu aikata laifi gaggawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kungiyar kare hakkin dan adam SERAP ta kai karar Najeriya gaban Majalisar Dinkin Duniya kan rashin tsaro.

Ƙungiyar SERAP ta bukaci Sakatare Janar na Majalisar, António Guterres ya yi amfani da Mataki na 99 domin kai Najeriya Kwamitin Tsaro.

SERAP ta bukaci a hukunta Tinubu kan rashin tsaro
Kungiyar SERAP ta maka Tinubu kara a kotu Hoto: @OfficialABAT, @SERAPnigeria.
Source: Twitter

Hakan na cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta wallafa a shafinta na X a yau Lahadi 31 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

'Jirgi marar matuki zan nada': Sowore kan wanda zai ba ministan tsaro idan ya ci mulki

SERAP ta koka kan matsalar tsaro a Najeriya

SERAP ta ce matsalar rashin tsaro da take kara ta’azzara a Najeriya na nuna sace-sacen mutane kisa da kai hare-hare kan fararen hula.

Ta ce Najeriya na fuskantar wannan matsala a jihohi kamar Oyo Benue Borno Plateau Kaduna Zamfara da wasu yankuna na kasar daban-daban.

Mataki na 99 na yarjejeniyar Majalisar ya ce Sakatare Janar iya gabatar duk wani batu ga Kwamitin Tsaro idan yana ganin barazana ce ga zaman lafiya.

SERAP ta ce girman da dorewar rikicin na iya zama barazana ga zaman lafiya da tsaro na kasa da kasa na duniya baki daya.

Sanarwar ta ce:

"Karuwar matsalar rashin tsaro da take addabar Najeriya tare da munanan take-haƙƙin ɗan Adam na bayyana ne ta hanyar yawaitar garkuwa da mutane, kashe-kashe, hare-hare kan fararen hula, da kuma raba jama'a da muhallansu a Oyo, Benue, Borno, Plateau, Kaduna, Zamfara da wasu sassa daban-daban na ƙasar.
SERAP ta bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta dauki mataki kan Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya a yayin taro a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

SERAP ta ce matsalar Najeriya ba kawai ta cikin gida ba ce tana da tasiri a yankin Yammacin Afrika saboda hijirar ‘yan bindiga da makamai.

Kara karanta wannan

Gobarar titi: Yadda tsawaita rufe Hormuz ke 'daga likkafar man Najeriya a Indiya

Yadda ƴan bindiga ke kai hari a Najeriya

An bayyana cewa ‘yan bindiga sun kai hari makarantu a Oyo inda suka sace dalibai da malamai tare da kashe wani mataimakin shugaban makaranta daya.

An kuma ce a Benue an sace dalibai da masu tafiya domin rubuta jarrabawar shiga jami’a a yayin tafiya zuwa cibiyar jarrabawa sun faru nan.

An kuma samu rahoton bama-bamai a Maiduguri da suka kashe mutane da jikkata da dama tare da kai hare-hare kan sansanonin ‘yan gudun hijira mummuna.

SERAP ta kuma bukaci majalisar da ta yi bincike kare fararen hula da hukunta masu laifi tare da tabbatar da zaman lafiya a Najeriya gaggawa.

SERAP ta maka Tinubu, NCC a kotu

Mun ba ku labarin cewa karin kuɗin kira da data ta hukumar sadarwa ta ƙasa (NCC) ta yi, na ci gaba da jawo cece-kuce a ƙasar nan.

Ƙungiyar SERAP ta ɗauki matakin shari'a inda ta ƙalubalanci ƙarin a gaban babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja.

SERAP ta buƙaci kotun da ta hana aiwatar da ƙarin inda ta ce ya saɓawa doka kuma an yi shi ne ba bisa ƙa'ida ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.