'Yan Bindiga Sun Bude wa Sojojin Najeriya Wuta a Benue, An Samu Asarar Rayuka
- 'Yan bindiga da ake zargin makiyaya Fulani ne sun kashe mutane huɗu, ciki har da sojoji biyu, a harin da suka kai Ijaha Ikobi, Benue
- An ce 'yan bindigar sun yi wa sojojin kwanton bauna a lokacin da suka kai dauki garin, kuma ana zargin sun kwace makamansu
- Shugaban ƙaramar hukumar Apa ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an fitar da gawarwakin sojojin da aka kashe daga yankin
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Benue - Ana zargi 'yan bindiga sun kashe mutane huɗu, ciki har da sojoji biyu, a garin Ijaha Ikobi da ke ƙaramar hukumar Apa a jihar Benue.
Wani mazaunin yankin mai suna Adakole ya bayyana cewa wasu makiyaya masu dauke da makamai sun kai hari garin a ranar Laraba.

Asali: Twitter
'Yan bindiga sun kashe sojoji 2 a Benue
Jaridar Punch ta rahoto Adakole yana cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:30 na daren jiya (Laraba). Mu dai mun ji yo karar harbe-harbe a cikin kauyen.
“Wasu sojoji da suka amsa kiran gaggawa sun fada komar Fulani, domin sun shirya masu kwanton bauna, kamar sun san za su zo, inda suka kashe sojoji biyu."
Ya ce daga cikin mazauna garin da suka rasa rayukansu akwai Ocheje Ngbede Sani da Aduba Paul Ogboyi, kuma ya zargi makiyayan da kwace makaman sojojin da suka kashe.
Shugaban ƙaramar hukumar Apa, Adam Ogwola, ya tabbatar da faruwar lamarin a tattaunawarsa da manema labarai ta wayar salula a ranar Alhamis.
Ciyaman ya tabbatar da kisan sojoji 2
Shi ma Adam Ogwola ya tabbatar da cewar 'yan bindigar da ake zargin makiyaya ne sun farmaki garin da misalin ƙarfe 3:30 daren Laraba.
Ogwola ya ce:
“Na samu kira cewa an kai hari a garin Ikobi da ke cikin ƙaramar hukumar Apa, amma lokacin da na kira wasu mutane daga can, ban same su ba.
“Daga baya sai na ji cewa sojoji biyu sun mutu, sannan da safe aka gano gawarwakin wasu fararen hula biyu.”
Yayin da yake bayyana cewa yanzu al’amura sun dan lafa, Ogwola ya ce an tura karin dakarun soji da 'yan sanda zuwa yankin domin tabbatar da tsaro.

Asali: Twitter
An fitar da gawarwakin sojojin daga yankin
Ya ce an riga an birne mutanen da aka kashe, yana mai cewa:
“Saboda al’adar mutanenmu, ba a ajiye gawar da 'yan bindiga suka kashe a dakin ajiyar gawa. Yanzu muna fuskantar hare-haren makiyaya sosai, don haka gawa ba ta wuce awa 24.
“Don haka an riga an birne su, yayin da aka fitar da gawarwakin sojojin daga yankin, amma ban san ko an kai su dakin ajiyar gawa na Ugbokpo ko na Makurdi ba.”
Da aka tuntubi kakakin rundunar Operation Whirl Stroke na sojoji, Kyaftin Lawal Osabo, bai ɗaga kiran waya ba.
Haka zalika, kiran da aka yi wa kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Catherine Anene, ya ƙi shiga, kuma ba ta mayar da saƙon da aka tura mata ba.
'Yan bindiga sun kashe sojoji a Benue
A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kai hari a wasu kauyukan Benue, inda suka kashe mutane biyar, ciki har da sojoji biyu.
An kai harin ne a ƙauyukan Mgbaigbe da Mbaitye, inda maharan suka yi wa sojojin da ke sintiri kwanton ɓauna, sannan suka hallaka fararen hula.
Shugaban ƙungiyar Mdzou U Tiv, Iorbee Ihagh, ya bukaci mazauna yankin da su kare kansu, yana zargin makiyaya Fulani da yunƙurin mamaye ƙasar Tibi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng