Sojoji Sun Fadi Sunan Wanda Ya Hada Kai da Boko Haram Wajen Kai Musu Hari a Borno
- Rahotanni sun bayyana cewa wasu sojoji na tserewa daga sansaninsu a Borno bayan harin Boko Haram da ya yi ajalin sojoji biyar a Marte
- Majiyoyin tsaro sun ce 'yan ta'addar sun ƙona sansanin soja, sun kwashe makamai da motoci, wanda ya tilasta wasu sojoji ajiye aiki
- An zargi wani jami'in CJTF da mai suna Sharu da cin amana, wanda ake zargin shi ya jagoranci 'yan ta'addar suka kai wa dakarun sojojin hari
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Borno - Rahotannin da muka samu na nuni cewa da wasu sojojin Najeriya na tserewa daga sansanoninsu bayan harin 'yan ta'addar Boko Haram.
Mun rahoto cewa Boko Haram ta sake kai hari sansanin sojoji a ranar Litinin a Marte, jihar Borno, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji biyar.

Asali: Facebook
Borno: Sojoji sun fara tserewa daga sansanoninsu
Jaridar Punch ta ce 'yan Boko Haram sun kai hari kan sansanin sojin, inda suka galabaita sojojin da ke bakin aiki, suka kwashe makamai, tare da guduwa da motocin yaki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyin soji, da suka yi magana a ranar Talata bisa sharadin sakaya sunansu, sun ce wasu daga cikin sojojin da harin ya rutsa da su sun tsere daga sansanoninsu, sun koma garuruwansu.
Ɗaya daga cikin majiyoyin ya ce:
"Yayin farmakin, sun ƙona komai. Sun lalata dukkan kayan aikinmu kuma sun kwashe makamai. Har ma sun tafi da motar kwamandanmu. Duk sababbin baburan da aka ba mu sun kwashe su.
"Wasu sojoji sun ajiye makamansu, sun ce aikin ya fita daga ransu. Sun fara komawa ƙauyukansu. Ɗaya daga cikinsu, wanda muke kira Dangwari, yana daga cikin waɗanda suka tafi."
Ana zargin jami'in CJTF ya sayar da sojoji
Wata majiyar kuma ta yi zargin cewa 'yan ta'addar sun samu nasara a farmakin da suka kai masu saboda cin amana daga wani jami'insu.
Jaridar MSN ta rahoto majiyar sojin tana cewa:
"Wani jami'in rundunar hadin gwiwa ta CJTF, wada muka amince da shi, ya ci amanarmu. Shi ne ya jagoranci 'yan ta'addar suka kawo mana hari sansaninmu. Sunansa Sharu. Yana kusa da sansaninmu kuma ana ɗaukar sa a matsayin wani jigo a rundunar."
Ya ƙara da cewa mazauna yankunan da ke kewaye da sansanin sun tsere sun bar gidajensu zuwa wasu garuruwan kamar Dikwa, Lukumani, da Mafa, saboda tsoron ƙarin hare-hare.

Asali: Twitter
Kwamandan soji ya yi martani kan farmakin
Kwamandan rundunar Operation Hadin Kai ta Arewa-maso-Gabas, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar, ya danganta ƙaruwar hare-haren 'yan ta'adda a jihar Borno da rashin zaman lafiya da ke gudana a yankin Sahel.
Manjo Janar Abdulsalam, ya bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai a Maiduguri, a ranar Talata, 13 ga Mayu.
Ya lura cewa tabarbarewar tsaro a ƙasashen Sahel da ke makwabtaka da Najeriya ya haifar da shigowar makamai cikin Najeriya, wanda ya ƙara tsananta rashin tsaro a Arewa-maso-Gabas.
Duk da halin da ake ciki, kwamandan ya ce rundunar sojin Najeriya na da yakinin samun nasara a yaƙin da take yi.
Boko ta dawo a Borno
Boko Haram ta dawo da karfi a jihar Borno bayan tsawon wani lokaci na lafawar ayyukansu, wanda ya janyo hankalin jama'a da sojoji.
Rashin zaman lafiya a yankin Sahel da makwabtaka ya taimaka wajen samun makamai da 'yan ta'adda suka shigo da su Najeriya.
Wannan ya kara tsananta matsalar tsaro a Borno, inda Boko Haram ta kai hari sansanonin sojoji da dama, kamar harin da aka kai a Marte wanda ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji biyar.
Wasu jami'an tsaro na zargin cin amana da jagorantar 'yan ta'adda daga cikin rundunar hadin gwiwa ta CJTF.
Wannan dawowa ta Boko Haram ta sanya wasu sojoji tserewa daga sansanoninsu, wanda ke jefa yankin cikin mawuyacin hali.
Boko Haram ta kwace makaman tirilioyin Naira
A wani labarin, mun ruwaito cewa, d'an majalisa daga Filato, Yusuf Gagdi, ya bayyana cewa Boko Haram sun ƙwace makaman sojoji da kuɗinsu ya kai tiriliyanin Naira.
Ya ce majalisar dokoki ta ware makudan kuɗaɗe don sayen makamai da motocin yaƙi, amma 'yan ta'adda na ci gaba da ƙwace su ba tare da wata matsala ba.
Hon. Gagdi ya yi gargaɗi cewa idan gwamnati ba ta ɗauki matakan da suka dace ba, 'yan Najeriya za su iya tashi tsaye don kare kansu da dukiyoyinsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng