Operation Whirl Stroke sun kai hari a Taraba da Benuwai, sun yi ram da Mai sace mutane

Operation Whirl Stroke sun kai hari a Taraba da Benuwai, sun yi ram da Mai sace mutane

Hedikwatar tsaro ta fitar da jawabi cewa Dakarun sojojin Operation Whirl Stroke sun lallasa wasu miyagun ‘yan bindiga a wani hari da su ka kai tsakanin jihohin Benuwai da Taraba.

Sojojin kasan da aka ajiye a garin Gbise da ke cikin karamar hukumar Kasina Ala, jihar Benuwai da wata bataliyar sojoji da ke jihar Taraba, sun hada-kai, sun kai wani farmaki.

Rundunar sojojin sun kai wa ‘yan bindiga hari ne a safiyar ranar Litinin a garuruwan Rafin Kada da ke cikin Wukari da kuma Yojaa a karamar hukumar Donga, duk a jihar Taraba.

Kamar yadda jawabin da aka fitar a yau, 30 ga watan 2020, ya nuna, sojojin sun yi kicibis da sojojin kabilar Tib da ke tada kayar baya a kauyen Che Jukun.

Wadannan mayaka sun budawa sojojin wuta bayan sun yi ido biyu, amma nan-take dakarun na Najeriya su ka koyawa tsagerun hankali, su ka kashe mutum hudu daga cikinsu a farat daya.

Haka zalika wasu daga cikin mayakan kabilar ta Tibi sun tsere da raunin bindiga a jikinsu.

KU KARANTA: Boko Haram: Sai an biya Dalolin kudi kafin a fito da wadanda aka tsare

Operation Whirl Stroke sun kai hari a Taraba-Benuwai, sun yi ram da Mai sace mutane
Shugaban sojojin kasan Najeriya
Asali: Twitter

“Daga cikin kayan da aka karbe akwai bindigogi biyu, casbi 55 na harsashe mai tsawon milamita 5.56, casbi 117 na harsashe mai tsawon milsmita 7.62, wayoyin salula 3, casbin harsashen bindigar AK 47.”

Sauran kayan ‘yan bindigan da aka karbe ba su tsaya a nan ba, akwai: “Babura biyu, kayan sojoji guda, takardar aikin jami’in kungiyar Peace Corps da sunan wani Anyor Fedelis da kuma wasu sarkoki.”

A wani labarin kuma, sojoji sun kama wani wanda ake zargi da laifin garkuwa da mutane a yankin Zaki Biam a jihar Benuwai.

Kobo Ishor wanda aka fi sani da Lesser, yaron Marigayi Orjondu ne wanda su ka addabi yankin. Mutanen gari ne su ka kai kukan ta'adin da Lesser ya ke yi masa a gaban jami'an tsaro.

Ana sa rai da zarar an gama yi masa tambayoyi, a mika sa gaban ‘yan sanda domin a shigar da shi kotu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel