NDLEA Ta Kama Basaraken Arewa da Wasu Mutum 10 Bisa Zargin Safarar Miyagun Kwayoyi

NDLEA Ta Kama Basaraken Arewa da Wasu Mutum 10 Bisa Zargin Safarar Miyagun Kwayoyi

  • Hakimin garin Gidan Abba da ke karamar hukumar Bodinga ta jihar Sokoto ya shiga hannun hukuma
  • Hukumar NDLEA ta kama Abubakar Ibrahim da wasu mutum 10 kan zargin fataucin miyagun kwayoyi
  • Kamun da jami'an hukumar hana fataucin miyagun kwayoyin suka yi a fadin jihohi bakwai ya yi sanadiyar kama haramtattun kwayoyi daban-daban

Jami’an hukumar hana fatauci da shan miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta kama hakimin garin Gidan Abba da ke karamar hukumar Bodinga a jihar Sokoto, Abubakar Ibrahim mai shekaru 38 kan fataucin kwayoyi.

Kakakin hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya bayyana a ranar Lahadi, 30 ga watan Oktoba, a Abuja, cewa an kama Ibrahim da ganyen wiwi mai nauyin kilo 3 da kuma kwayoyin exol-5 guda 4,000, Daily Trust ta rahoto.

Jami'an NDLEA
NDLEA Ta Kama Basaraken Arewa da Wasu Mutum 10 Bisa Zargin Safarar Miyagun Kwayoyi Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Hakimin yana daga cikin mutum 11 da aka kama a tsakanin wasu ayyuka da suka kai jami’an NDLEA ga samo miyagun kwayoyi daban-daban a gadin jihohi bakwai.

A cewarsa, a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Ikeja Lagos, jam’an NDLEA da ke aiki da kamfanin shigo da kaya na SAHCO sun kama kwalaye 15 dauke da kwayoyin Tramadol.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Daily Post ta rahoto cewa an shigo da miyagun kwayoyin ne daga Dubai, UAE da Karachi, Pakistani a ranar Laraba, 26 ga watan Oktoba.

Babafemi ya ce:

“Yayin da kwalaye 10 na kwayoyin Tramadol 225mg suka fito daga Dubai a jirgin Ethiopia, kwalaye hudu na 100mg da kwali daya na Tramadon 22mg sun fito daga Karachi, Pakistani a wani jirgi daban na Ethiopia."

Katsina: ‘Yan Sanda Sun Yi Ram da Gagararren Dilallin Kwayoyi

A wani labarin kuma, mun kawo cewa a kalla buhuna 27 na busasshen ganye da aka boye cikin garri wanda ake zargin tabar wiwi cewa tare da sunki 31 na kwayar Exol tare da sunki 30 na Tramadol ‘yan sandan jihar Katsina suka kama.

A wurin kamen, an damke gagararren matashi da ya shahara wurin dillancin wiwi mai suna Ukashatu Idris na kauyen Kiyaki a karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah a wata tattaunawa da yayi ga manema labarai a hedkwatar rundunar dake Katsina, yace an kama Idris a ranar Talata, 25 ga watan Oktoba bayan samun bayanan sirri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel