Bayanai Sun Fito kan 'Bidiyon Lalata' da Ake Zargin Wani Sanata na Jin Dadinsa da Wata Mata

Bayanai Sun Fito kan 'Bidiyon Lalata' da Ake Zargin Wani Sanata na Jin Dadinsa da Wata Mata

  • Kafafen sada zumunta sun ɗauki zafi da aka fara yaɗa wani bidiyon lalata wanda ake tunanin wani sanatan Najeriya ne
  • Bidiyon ya nuna wani babban mutum cikin shiga ta kamala ya shiga yanayin soyayya da wata mace har da sumbata da rungumar juna
  • Majalisar Dattawa ta musanta zargin cewa sanata mai ci ne a bidiyon, inda ta ce an daɗe ana yaɗa shi a kafafen sada zumunta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta wanda ya nuna wani mutumi da mace suna jin daɗinsu a ofis ya tayar da ƙura, wasu na ganin sanata mai ci ne.

Faifan bidiyon mai tsawon mintuna biyu da daƙiƙa 10 ya nuna wani mutumi da jama'a ke zargin sanata ne, yana jin daɗinsa da wata mace, suna sumbatar juna a ofis.

Msjalisar Dattawa.
Majalisar dattawa ta nesanta kanta da wani bidiyo da ake dangantawa da sanata Hoto: @SenateNGR
Asali: Facebook

Bidiyon da ake zargin na wani sanata ne

Shafin Obident Word ya wallafa bidiyon wanda ya girgiza kafafen sada zumunta jiya Talata a manhajar X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Dubi Sanata da budurwarsa ta gefe suna jin dadinsu a cikin harabar majalisar kasa. Gobe ​​wasu wawaye marasa amfani za su zo nan suna kare 'yan siyasa.

Wasu daga cikin masu amfani da kafafen sada zumunta sun yi ikirarin cewa an dauki bidiyon a ofishin wani sanata da ke aiki yanzu haka a Majalisar Dattawa a Abuja.

Bidiyon dai ya nuna mutumin sanye da gilashi yana soyayya da wata mace, suna sunbatar juna da rungumar juna a cikin wani ɗaki da aka bayyana da ofis.

Da gaske sanata ne a bidiyon?

Majalisar Dattawan Najeriya ta musanta zargin da ke cewa wani sanata mai ci ne ke cikin bidiyon iskancin da ake kara yadawa a kafafen sada zumunta.

Da yake mayar da martani, kakakin majalisar dattawa kuma shugaban kwamitin hulda da jama’a, Sanata Yemi Adaramodu, ya bayyana bidiyon a matsayin tsohon abu mara tushe.

A rahoton Leadership, Adaramodu ya ce:

“Wannan ba bidiyon wani sanata ba ne mai ci. Wannan bidiyo na yawo tun kafin in zama sanata.”
"Ofishin da aka gani a cikin bidiyon ba ya kama da wani ofis da ke cikin Majalisar Dattawa. Zan iya bude muku ofisoshi 10 don ku kwatanta babu wani da ya yi kama da na cikin bidiyon."

Haka nan, rahoton Sahara Reporters ya goyi bayan ikirarin Adaramodu, inda ya bayyana cewa bidiyon tsoho ne an daɗe ana yaɗa shi a shekarun da suka wuce.

Waye a cikin bidiyon da ake surutu a kai?

Duk da haka, jama’a da dama a kafafen sada zumunta na ci gaba da nuna shakku tare da bukatar karin haske da bayyana gaskiya daga jami’an gwamnati.

Kawo yanzu ba a tabbatar da sunan namijin da ke cikin bidiyon ko matar da ke tare da shi ba.

Majalisa ta nanata cewa babu wata alaka da ta ke da ita da wannan bidiyon, tana kuma yi kira ga ‘yan kasa da su guji yada bayanan karya da aka kirkira a kafafen sada zumunta.

Majalisa ta damu da hare-haren Boko Haram

A wani rahoton, kun ji cewa Majalisar Dattawa ta nuna damuwa kan dawowar hare-haren Boko Haram a jihohin Borno da Yobe.

Majalisar ta buƙaci rundunar sojoji da ta sake tura dakarunta tare da kayan aiki na zamani zuwa jihohin Borno da Yobe da ke Arewa maso Gabas.

Majalisar ta ɗauki wannan matakin ne bayan amincewa da kudirin da Sanata Tahir Monguno, babban mai tsawatarwa ya gabatar

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262