Hotuna da Bidiyon shagalin Kamun diyar Sanata Sahabi Yau sun Dauka Hankali

Hotuna da Bidiyon shagalin Kamun diyar Sanata Sahabi Yau sun Dauka Hankali

  • Hotunan diyar Sanata Sahabi Ya'u tare da masoyinta kuma angonta, Muhammad Auwal sun matukar daukar hankali
  • Kyakyawar amarya Ummi ta yi shiga cikin kayan alfarma inda ta fito tas a gaban angonta da ya sha manyan kaya
  • An ga 'yan mata kyawawa, samari, 'yan uwan amarya da na angon suka cashewa duk don taya masoyan murnar babbar ranar

Kyawawan hotunan shagalin bikin kamun diyar Sanata Sahabi Yau da angonta Muhammad Auwal sun matukar daukar hankali.

Kyakyawar amarya Ummi Sahabi Yau ta yi shiga mai matukar daukar hankali a yayin da take shirin auren masoyinta kuma rabin ranta Muhammad Auwal.

Diyar Sanata
Hotuna da Bidiyon shagalin Kamun diyar Sanata Sahabi Yau sun Dauka Hankali. Hoto daga @fashionseriesng
Asali: Instagram

A hotuna da bidiyon da Legit.ng Hausa ta tattaro muku daga @fashionseriesng, sun matukar kayatarwa inda aka ga 'yan uwa, abokan arziki da masoyansu duk sun halarci wurin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Bidiyoyin Shagalin Kamun Kyakkyawar Diyar Sanata Sahabi

Kyawawan Hotuna da Bidiyo Daga Kamun Kabiru Aminu Bayero da Tsuleliyar Amaryarsa

A wani labari na daban, kyawawan hotuna da bidiyoyin wurin kamun ango Kabiru Aminu Bayero da zukekiyar amaryarsa, Aisha Ummarun Kwabo sun matukar kayatar da jama'a.

Biki tuni dai ya kankama inda ake hango ranar daurin aure, Juma'a, 26 ga watan Augustan 2020 a jihar Sokoto.

A daren Laraba ne aka fara da shagalin bikin auren inda kamun da aka yi ya matukar kayatarwa ganin yadda kyakyawar amaryar ta fito shar cikin shiga ta alfarma da kwalisa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel