Za Su Sha Jar Miya: NAHCON Ta Fadi Nau'in Abinci da Za a Rika ba Alhazai a Madina

Za Su Sha Jar Miya: NAHCON Ta Fadi Nau'in Abinci da Za a Rika ba Alhazai a Madina

  • Hukumar NAHCON ta tabbatar da cewa mahajjatan Najeriya za su ci abinci mai gina jiki da dandanon gargajiya yayin Hajjin 2025 a Madina
  • Hukumar ta kafa tsari mai tsauri na bincike da sa ido kan girke-girke, domin tabbatar da tsafta da hana amfani da kayan da suka lalace
  • An tabbatar da cewa ’yan Najeriya ne ke girki a gidajen abinci bakwai na Madina, yayin da aka haramta amfani da wasu sinadarai a abincin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Madina- Hukumar Hajji ta kasa (NAHCON) ta tabbatar da cewa mahajjatan Najeriya da ke gudanar da aikin hajjin 2025 za su ci abinci mai inganci da gina jiki.

NAHCON ta bayyana cewa ta dauki tsauraran matakan duba inganci da tsafta yayin zaben gidajen da za su rika dafawa mahajjatan abinci a Madina.

Hukumar NAHCON ta ba da tabbacin cewa alhazai za su ci abinci mai gina jiki
Shugabannin hukumar NAHCON yayin da suke tattauna wa a Saudiyya. Hoto: @nigeriahajjcom
Asali: Twitter

Alhazan Najeriya 17,000 sun isa Saudiya

Shugaban kwamitin ciyar da mahajjata a Madina, Alhaji Abdullahi Kabir, ne ya bayyana hakan a sanarwar da jami'in hulda da jama'a na kwamitin ya fitar ranar Juma'a, inji Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alhaji Abdullahi, ya bayyana hakan ne yayin ziyarar duba gidajen girki bakwai da ke da alhakin ciyar da mahajjata fiye da 17,000 da suka isa birnin mai tsarki.

Jami’in hulɗa da jama’a na kwamitin, Malam Ahmad Muazu, ya ruwaito Alhaji Abdullahi yana cewa:

“Yayin da mahajjata sama da 17,000 daga Najeriya suka iso Madina, NAHCON ta kafa tsari mai ƙarfi na sa ido don tabbatar da daidaito da inganci a ciyar da alhazan."

Alhazai za su samu abinci mai gina jiki

Alhaji Abdulahi ya bayyana cewa hukumar NAHCON ta bi matakai daban-daban wajen zaben gidajen dafa abincin, da suka hada da inganci, tantance kayan abinci, da sauransu, don tabbatar da samar da abinci mai gina jiki.

Shugaban kwamitin ya kara da cewa:

“An duba kwanan watan da kayayyakin za su lalace, kama daga daga kayan kamshi zuwa abinci da aka adana, inda NAHCON ke da ƙa'ida mai tsauri na hana amfani da kayan da suka lalace,” in ji shi.

NAHCON ta kuma hana amfani da sinadarai masu illa ga jiki, inda ta buƙaci amfani da sinadarai na gargajiya da aka saba da su domin ya yi daidai da ingancin abincin Najeriya.

A cewar Kabir, gidajen girki bakwai da aka tantance sune: Africana Home Restaurant, Amjad Alghraa, Al-Andalus, Mawasim Khairat, Na’a Azad, Zowar Muktara da Kabala Catering.

Hukumar NAHCON ta ce alhazan Najeriya za su samu abinci mai gina jiki a Saudiyya
Maniyyata aikin Hajji daga Najeriya na shiga jirgi domin jigilarsu zuwa Saudiya. Hoto: @nigeriahajjcom
Asali: Facebook

An hana amfani da robobi marasa inganci

A wani muhimmin mataki, an tabbatar da cewa ’yan Najeriya ne ke girki da aiki a cikin wadannan gidajen girki, domin tabbatar da cewa komai ya yi daidai da dandanon gida.

A wani taro da masu ba da abinci, jagoran NAHCON na Madina, Alhaji Abdulkadir Oloyin, ya tattauna batun kayan da ake zuba abinci yayin da ya fitar da muhimmiyar sanarwa.

“Ba za mu yarda da amfani da robobin zuba abinci marasa inganci ba, ba zai yiwu ba,” inji Oloyin, yayin da ya gargadi masu rabon abincin.

Ya umurce su da su dinga amfani da irin robobin zuba abinci kala ɗaya domin kare lafiyar abinci da kuma saukaka wa mahajjata wajen cin abinci.

Sunayen kamfanonin da ke jigilar alhazai

A wani labarin, mun ruwaito cewa, fadar shugaban kasa ta zaɓi kamfanonin jiragen Air Peace, Fly-Nas, Max Air da UMZA don jigilar alhazai a Hajjin 2025.

Kwamitin gwamnati mai mambobi 32 daga hukumomi daban-daban ne ya gudanar da tantancewa, aka zabi hudu cikin kamfanoni 11 da suka nuna sha'awar aikin.

Hukumar NAHCON na bayyana cewa ta kamalla sanya hannu kan duk wata yarjejeniyar aikin Hajjin bana tsakanin Najeriya da Saudiyya a birnin Jiddah.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.