Dan Majalisa Ya Yi Hangen Nesa, Ya Fadi Hanyar Magance Rashin Tsaro

Dan Majalisa Ya Yi Hangen Nesa, Ya Fadi Hanyar Magance Rashin Tsaro

  • Ɗan majalisar wakilan Najeriya daga jihar Legas, Babajimi Benson, ya yi magana kan rashin tsaron da ake fama da ita
  • Babajimi Benson ya bayyana cewa ba ƙananan hukumomi ƴancin cin gashin kansu zai taimaka wajen magance rashin tsaro
  • Ɗan majalisar ya nuna cewa ƙananan hukumomi suna da matuƙar muhimmanci kuma za su taka rawa wajen kawo ƙarshen rashin tsaro

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Ɗan majalisar wakilai, Babajimi Benson, ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita.

Babajimi Benson ya danganta ci gaba da taɓarɓarewar tsaro a Najeriya da ƙin aiwatar da tsarin ƴancin cin gashin kai na ƙananan hukumomi.

Babajimi Benson
Babajimi Benson ya samo mafita kan rashin tsaro Hoto: @IamJimiBenson
Asali: Twitter

Shugaban kwamitin taro na majalisar wakilan, ya bayyana haka ne cikin wata hira da jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan majalisa ya yi magana kan rashin tsaro

Babajimi Benson, wanda ke wakiltar mazaɓar Ikorodu ta tarayya a jihar Legas, ya bayyana cewa ƙananan hukumomi masu cin gashin kansu za su fi dacewa wajen magance matsalolin tsaro a matakin farko.

Ɗan majalisar ya ce ƙananan hukumomi sun fi dacewa da aiwatar da hanyoyin warware matsalar tsaro ba ta hanyar yaƙi ba, irin su tattara bayanan sirri, ƴan sandan al’umma, tallafawa matasa, da shirin sauya tunanin masu tsatstsauran ra'ayi.

"Ƙin aiwatar da ƴancin cin gashi kai na ƙananan hukumomi da wasu gwamnonin jihohi ke yi, duk da goyon bayan da ya samu daga kundin tsarin mulki da kuma umarnin shugaban ƙasa, na daga cikin manyan abubuwan da ke ƙara ta’azzara matsalar tsaro a ƙasar nan."

- Babajimi Benson

Ya buƙaci a ba ƙananan hukumomi ƴanci

Benson ya ƙara da cewa mayar da ikon kuɗaɗen ƙananan hukumomi a hannun gwamnoni na ci gaba da haifar da nauyi a kan gwamnatocin tarayya da na jihohi, sannan yana raunana tsarin tsaron ƙasa gaba ɗaya.

Ya dage cewa ba da ƴancin cin gashin kai ta fannin kuɗi da na gudanarwa ga ƙananan hukumomi zai taimaka matuƙa wajen inganta harkar tsaro a cikin gida.

Babajimi Benson
Babajimi Benson ya yi magana kan rashin tsaro Hoto: @IamJimiBenson
Asali: Twitter
"Ƙananan hukumomi su ne mafi kusa da talakawa, kuma su ne hanyoyi mafi inganci wajen aiwatar da hanyoyin da ba su da nasaba da yaƙi wajen magance matsalar tsaro."
"Idan ƙaramar hukuma tana da ƴancin gashin kanta kan kuɗi da ikon gudanarwa, za ta iya tara kuɗi don shirye-shiryen tsaro, tattara bayanan sirri, ƴan sanda na al’umma, da kuma samar da ayyukan yi da tallafawa masu sana’o’i."
"Haka kuma za ta zama hanya wajen sauya tunanin matasa daga ta’addanci. Ci gaba da mayar da dukkan iko da kuɗin ƙananan hukumomi a hannun gwamnatocin tarayya da jihohi, na ƙara musu nauyi da kuma raunana ginshikin tsaron ƙasa tun daga tushe."

Babajimi Benson

Ƴan ISWAP sun kai hari a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan ta'addan ISWAP sun kai harin ta'addancina jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabas.

Ƴan ta'addan sun hallaka manoma da masunta fiye da guda 20 a ƙaramar hukumar Kukawa ta jihar.

Mayaƙan na ISWAP sun kashe manoman ne bayan sun zarge su da yin aiki tare da ƴan ta'addan Boko Haram.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng