Shugaba Tinubu Ya Karowa Sojoji Jirage bayan ISWAP Ta Matsa da Hare Hare
- Shugaban kasa, Bola Tinubu ya kaddamar da sababbin jiragen helikwafta guda biyu domin yaki da matsalar tsaro a Najeriya
- Haka kuma rundunar sojin sama ta Najeriya za ta karbi karin jirage 49 daga yanzu zuwa shekarar 2027 don bunkasa aikin tsaro
- Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya wakilci Tinubu a wajen kaddamar da sababbin jiragen masu saukar unguku
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da sababbin jiragen helikwafta guda biyu ga dakarun rundunar sojin saman Najeriya.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da ya wakilci Tinubu ne ya kaddamar da jiragen a daidai lokacin da 'yan ta'adda ke kara kai hare-hare a jihar Borno.

Asali: Facebook
Channels TV ta ruwaito cewa an samar da sababbin jiragen ne domin a kara zaburar da dakarun sojin saman kasar nan wajen yakar 'yan ta'adda.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya kaddamar da sababbin jiragen yaki
TVC News ta wallafa cewa kaddamar da jiragen ya zo ne daidai da cikar shekaru 61 da kafuwar rundunar sojin saman Najeriya.
An samar da jiragen helikwafta biyu, NAF544 da NAF545, ne domin karfafa karfin rundunar sojin sama wajen yaki da matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta.
Kaddamar da sababbin jiragen ya zo kwanaki kadan bayan kungiyar yan ta'addan ISWAP ta dauki alhakin kai hare-hare zuwa sansanin sojoji a jihar Borno.
Shugaban kasa Tinubu zai karo jiragen yaki
Shugaban Hafsoshin Rundunar Sojin Sama, Air Marshal Hassan Abubakar, ya bayyana cewa rundunar za ta karbi karin jirage 49 nan da shekarar 2027.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya kaddamar da sababbin jiragen helikwafta nau’in 109S Trekker guda biyu a Abuja, a ranar Alhamis.

Asali: Facebook
Ya ce daga shekarar 2024 zuwa yanzu, rundunar sojin sama ta karbi jirage guda tara zuwa cikin jerin kayayyakin aikin ta.
Daga cikinsu har da jiragen yaki nau’in 4t, 129, jiragen King Air 360 guda uku, da kuma jiragen helikwafta nau’in Agusta 109 Trekker guda biyu da aka kaddamar.
Ya kara da cewa:
“Dangane da kudurin Shugaban Kasa na tabbatar da tsaron Najeriya, rundunar sojin sama ta kammala shiri don karbar karin jirage 49 cikin shekaru biyu masu zuwa. Wannan ya hada da karin jiragen Agusta 109 Trekker guda 10, jiragen yaki nau’in A-1 Zulu guda 12, jiragen yaki da na saukar kasa nau’in 4m, 346 guda 20, da kuma jiragen jigilar kaya na CASA 295 Million guda uku.”
Nadin Tinubu ya jawo zanga-zanga
A baya, kun ji cewa kungiyar APC ta Arewa ta Tsakiya ta bayyana goyon bayanta ga nadin Cyril Tsenyil a matsayin Darakta Janar na Hukumar Raya Yankin Arewa ta Tsakiya (NCDC).
Wannan na zuwa ne a yayin da ta yi watsi da zanga-zangar da wasu ke yi kan wannan nadin, tana mai cewa 'yan adawa ne suka dauki nauyin mutanen don kawo cikas ga Filato.
Shugaban kungiyar, Saleh Zazzaga, ya bayyana ya yi nuni da cewa duk dan yankin ba zai yi adawa da nadin Tsenyil ba saboda manufarsa ta ci gaban APC da yankinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng