'Dan Majalisa Ya Koka da Rashin Tsaro, Ya Fadi Barnar da 'Yan Bindiga Suka Yi a Mazabarsa
- Ɗan majalisar wakilai daga jihar Zamfara, Aminu Sani Jaji, ya koka kan yadda ƴan bindiga ke cin karensu babu babbaka a mazaɓarsa
- Aminu Sani Jaji wanda ke wakiltar Kaura Namoda/Birnin Magaji ya bayyana cewa ƴan bindiga sun addabi mutanen mazaɓarsa da hare-hare
- Ya nuna cewa mutane da dama suna tsare a hannun ƴan bindiga bayan sun yi garkuwa da su zuwa cikin daji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Wani ɗan majalisar wakilai daga jihar Zamfara, Aminu Sani Jaji, ya koka kan taɓarɓarewar matsalar tsaro a mazaɓarsa.
Aminu Sani Jaji ya bayyana cewa sama da mutum 200 daga cikin mutanen mazaɓarsa ƴan bindiga suka sace a cikin jerin hare-haren da suka addabi yankin a makonnin baya-bayan nan.

Asali: Original
Aminu Sani Jaji wanda yake wakiltar Kaura Namoda/Birnin Magaji, ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a majalisar tarayya ranar Laraba, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɗan majalisa ya koka kan rashin tsaro
Ɗan majalisar ya ce yankin wanda a baya yake cike da zaman lafiya, yanzu ya koma filin faɗa, inda al’umma ke rayuwa cikin tsoron hare-hare, sace-sace da kisa.
“A mazaɓata kaɗai, sama da mutum 200 ƴan bindiga suka sace. Mako biyu da suka gabata, an sace mutane 60 a ƙauyen Banga. Daga ciki, an kashe mutum 10 saboda al’ummar ƙauyen ba su iya tara kudin fansa Naira miliyan 30 da masu garkuwa suka buƙata ba."
"Yayin da muke cikin jimami, sai ga wasu 25 an sake sace su daga ƙauyen Gabake. Har jiya ma, sababbin hare-hare sun sake faruwa a Kungurki."
- Aminu Sani Jaji
Da aka tambaye shi kan yiwuwar ayyana dokar ta-baci a jihar Zamfara, ya nuna cewa baya goyon bayan hakan.
“Idan za a ayyana dokar ta ɓaci a Zamfara, to ya kamata a ayyana ta a sama da jihohi 20. Matsalar rashin tsaro matsala ce ta ƙasa baki ɗaya, ba ta yanki ɗaya ba ce."
- Aminu Sani Jaji

Asali: Facebook
Aminu Sani Jaji ya yi kira ga gwamnatin tarayya
Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ƙara zage damtse, ba kawai domin jihar Zamfara ba, har ma da dukkan sassan ƙasar nan da ke fama da rikice-rikicen da ke da nasaba da makamai.
“Wannan ba siyasa ba ce a yanzu. Bala’i ne babba. Idan muka kasa ɗaukar mataki yanzu, lamari zai mamaye gaba ɗaya ƙasar."
- Aminu Sani Jaji
Sojoji sun ragargaji ƴan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun bi ƴan ta'adda har cikin daji, suka yi artabu mai zafi a jihohin Sokoto da Zamfara.
Dakarun sojojin sun kutsa cikin dazukan da ke sassan daban-daban na jihohin inda suka lalata sansanonin ƴan ta'adda masu yawa.
Jami'an tsaron sun kuma kashe wasu daga cikin ƴan ta'addan tare da ƙwato makamai masu tarin yawa a hannunsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng