Ana tsaka da Jimami, Ƴan ISWAP Sun Sake Kai Kazamin Hari kan Sojojin Najeriya

Ana tsaka da Jimami, Ƴan ISWAP Sun Sake Kai Kazamin Hari kan Sojojin Najeriya

  • Ƴan ta'addan ISWAP sun sake kai farmaki sansanin sojoji a ƙaramar hukimar Kala-Balge da ke jihar Borno da tsakar dare
  • An ruwaito cewa maharan sun kutsa sansanin sojin ne da misalin karfe 12:00 na daren yau Talata, sun kashe sojoji biyar
  • Duk da rundunar sojin Najeriya ba ta ce uffan ba kan sabon harin, amma majiyoyi sun ce ƴan ta'addan sun tafka ɓarna mai girma

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Ƴan ta'addan kungiyar ISWAP sun sake kai kazamin farmaki sansanin sojojin Najeriya a ƙaramar hukumar Kala-Balge ta jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa akalla sojoji biyar ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu shida suka samu munanan raunuka a harin na ISWAP.

Taswirar Borno.
ISWAP ta sake kai farmaki sansanin sojoji a Borno, sun kashe jami'ai 5 Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Leadership ta tattaro cewa maharan sun mamayi sojojin da tsakar dare misalin karfe 12:00 na daren Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan ta'adda sun yi amfani da jirage a Borno

Ƴan ta'addan sun yi amfani da jiragen leƙen asiri marasa matuki wajen kaddamar da harin kan Bataliya ta 3 da ke Rann, hedikwatar karamar hukumar Kala-Balge.

Wannan hari ya biyo bayan wani makamancinsa da ƴan ta'adda suka kai a sansanin sojoji da ke New Marte.

A harin, maharan sun kashe sojoji da dama, sun lalata motocin yaki, sannan suka yi awon gaba da mugayen makamai.

Har ila yau ƴan ta'addan sun fatattaki mazauna yankin, wadanda suka gudu daga gidajensu domin tsira da rayukansu.

ISWAP ta ƙara kashe dakarun sojoji 5

Wata majiya da cikin jami'an tsaro ta bayyana cewa:

“Muna cikin tsananin rudani da firgici. Wannan sabon harin ya faru da misalin karfe 12:00 na dare. An kashe sojoji biyar, wasu shida kuma sun ji munanan raunuka.”

Wani mazaunin yankin, Babagana Modu ya yaba da jarumtakar dakarun sojojin, duk da cewa ‘yan ta’addan sun yi amfani da muggan makamai wanda ya tilasta sojojin ja da baya cikin dabaru.

Gwamna Zulum.
Yan ta'adda sun kara kashe sojoji a Borno Hoto: @ProfZulum
Asali: Facebook

Sojoji sun gwabza da mayaƙan ISWAP

Ya ce duk da ƴan ta'addan sun kai farmakin cikin shiri amma sojoji sun nuna jarumta da suka tare su aka yi ɗauƙi ba daɗi mai tsanani.

A gefe guda, dakarun Najeriya sun dakile wani yunkuri na ISWAP a Gajiram, hedikwatar karamar hukumar Nganzai, a ranar Litinin da dare, inda suka hana su shiga sansanin soji.

Har yanzu rundunar sojojin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance ba dangane da hare-haren da suka afku cikin sa’o’i 24 da suka gabata a jihar Borno.

Zulum ya yi Allah wadai da hare-haren ISWAP

A wani labarin, kun ji cewa gwamna Babagana Zulum, ya yi alhini da Allah wadai kan sababbin hare-haren da ƴan ta'addan Boko Haram/ISWAP suka kai a Borno.

Gwamna Zulum ya kuma yi jimami ga iyalan waɗanda abin ya rutsa da su, musamman waɗanda fashewar bam ɗin da aka binne ya shafa a titin Maiduguri-Damboa.

Farfesa Zulum ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin tarayya, sojoji da sauran hukumomin tsaro don dawo da zaman lafiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262