Atiku Ya Caccaki Tinubu da EFCC kan Yin Shiru bayan Kama Gudaji Kazaure

Atiku Ya Caccaki Tinubu da EFCC kan Yin Shiru bayan Kama Gudaji Kazaure

  • EFCC ta sake shiga zargin take hakkin bil’adama bayan kama tsohon dan majalisar wakilai, Gudaji Kazaure, ba tare da bayyana dalili ba
  • Ana zargin hukumar tarayyar ta cafke Gudaji Kazaure na da nasaba da sukar da yake yi wa gwamnatin Bola Tinubu kan yadda ake tafiyar da kasa
  • Atiku Abubakar ya caccaki EFCC da gwamnatin Tinubu, yana mai cewa suna kokarin hana masu sukar gwamnati 'yancin yin magana

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana damuwa kan yadda hukumar EFCC ke ci gaba da keta dokar kasa ta hanyar cafke mutane.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Atiku ya ce abin takaici ne ganin yadda EFCC ta kama hanyar tsoratar da masu sukar gwamnati.

Gudaji
Atiku ya yi magana kan kama Gudaji Kazaure. Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Twitter

Atiku Abubakar ya wallafa a X cewa an cafke tsohon dan majalisar wakilai, Muhammad Gudaji Kazaure a Kano aka kai shi Abuja ba tare da bayani ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku ya ce wannan lamari ya zama tamkar daukar doka a hannu, inda aka bar iyalai da lauyoyin Kazaure cikin duhu kan inda yake da kuma dalilin tsare shi.

Atiku: 'Kazaure na cikin masu sukar gwamnati'

Atiku Abubakar ya ce Gudaji Kazaure ya kasance daya daga cikin ’yan siyasar da ke sukar gwamnatin Bola Tinubu kan yadda ake tafiyar da al’amuran kasa, musamman tattalin da tsaro.

Ya ce tsare Gudaji Kazaure yana da alaka kai tsaye da irin sukar da yake yi wa gwamnati, yana mai cewa hakan yana nuni da kokarin dakile ’yancin fadin albarkacin baki a kasar nan.

A cewarsa,

“Gwamnatin da ke yin alaka da wadanda ake zargi da cin hanci, amma kuma take cafke masu sukar ta, ta nuna irin son kai da rashin adalci da ke cikinta karara .”

Atiku
Atiku ya bukaci bayani kan kama Gudaji Kazaure. Hoto: Hon. Muhammad Gudaji Kazaure
Asali: Youtube

EFCC ta na kara zubar da kimarta inji Atiku

Atiku ya kara da cewa dokar kasa ta Najeriya ta fayyace cewa ya kamata a gurfanar duk wanda aka kama cikin lokaci ko a sako shi, ba a ci gaba da rike shi ba tare da bayani ba.

Ya ce:

“Ko da akwai dalili na kama mutum, wajibi ne a bi doka.
Hukumar EFCC na da nauyin bayyana laifin da ake tuhumar mutum da shi. Amma abin takaici, suna rike mutane a boye ba tare da shari’a ba.”

Ya jaddada cewa irin wannan salon mulki da take hakkin dan Adam yana kara lalata tsarin dimokuradiyya da kuma karfafa rashin gaskiya a cikin gwamnati.

Atiku ya gargadi gwamnati da hukumar EFCC da su dakatar da wannan dabi’a, yana mai cewa ’yan Najeriya na kallon abin da ke faruwa kuma tarihi ba zai manta ba.

Atiku ya kira Tinubu ya yi aiki da kayan Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya kalubalanci Bola Tinubu kan hana shigo da kaya daga waje.

Atiku ya ce idan har Bola Tinubu da gaske ya ke wajen bunkasa amfani da kayan Najeriya ya kamata ya fara aiki da su da kan shi.

Rahoton Legit ya tabbatar da cewa Atiku Abubakar ya fadi haka ne bayan shugaba Bola Tinubu ya hana shigo da kayayyakin ketare da ake hada wa a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng