Tsaro Ya Caɓe a Ƙasa: Shugaba Tinubu Ya Tasa Manyan Hafsoshin Tsaro a Aso Villa

Tsaro Ya Caɓe a Ƙasa: Shugaba Tinubu Ya Tasa Manyan Hafsoshin Tsaro a Aso Villa

  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gana da hafsoshin tsaro a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja yau Juma'a, 16 ga watan Mayu 2025
  • Bola Tinubu ya gana da shugabannin tsaro ne a daidai lokacin da hare-haren ƴan ta'adda ke ƙaruwa musamman a yankin Arewa maso Gabas
  • Har kawo yanzu ba a bayyana makasudin wannan taro ba amma ana ganin ba zai rasa nasaba da taɓarɓarewar tsaro a ƴan kwanakin nan ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

State House, Abuja - Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawa da manyan hafsoshin tsaron kasar nan yayin da sha'anin tsaro ke ƙara taɓarɓarewa.

Shugaba Tinubu ya sa labule da shugabannin tsaron ne a fadar shugaban ƙasa da ke babban birnin tarayya Abuja yau Juma'a, 16 ga watan Mayu, 2025.

Shugaba Tinubu.
Bola Tinubu ya sa labule da hafsoshin tsaro da sufetan ƴan sanda a Abuja Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Hafsoshin tsaron da suka gana da Tinubu

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa wadanda suka halarci ganawar sun haɗa da babban hafsan hafsoshin tsaro na kasa, Janar Christopher Musa da shugaban rundunar sojin ƙasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran shugabannin tsaron da suka halarci zaman sune shugaban rundunar sojin sama na ƙasa, Air Marshal Hassan Abubakar da shugaban rundunar sojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla.

Bugu da kari, Sufeto Janar na rundunar 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya halarci taron tsaron a Abuja.

Duk da yake ba a yi cikakken bayani kan maƙasudin wannan taro ba, ana kyautata zaton ba zai rasa nasaba da yadda tsaro ke kara taɓarɓarewa a wasu sassan ƙasar nan, musamman a Arewa ba.

Me aka tattauna a taron Majalisar Tsaro?

Idan za ku iya tunawa a ƴan kwanakin nan, ƴan ta'addan Boko Haram da ISWAP sun zafafa ksi hare-hare a sansanonin sojoji a jihar Borno da ke Arewa maso Gabas.

An ruwaito cewa wasu 'yan ta'addan ISWAP sun fara kai hari sansanin sojoji da ke Karamar Hukumar Marte, da misalin 3.00 na safiyar Litinin da ta gabata.

Bayan haka, ƴan ta'addan sun sake kai hari sansanin sojoji da ke Rann, hedikwatar Karamar Hukumar Kala Balge da tsakar daren Talata.

Majiyoyi sun ce harin ya fara ne kimanin 12:00 na dare ranar Talata, inda ‘yan ta’addan suka mamaye sansanin da manyan makamai, The Nation ta ruwaito.

Ana ganin wannan hare-hare da ma wasu da ƴan ta'adda suka kai a sassan Najeriya na daga cikin dalilan da suka sa shugaban ƙasa ya kira taron majalisar tsaro ta ƙasa.

Najeriya ta sayo wa sojoji ƙarin makami

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya karkashin Bola Ahmed Tinubu ya sayo ƙarin makamai domin kawo ƙarahen ayyukan ta'addanci a Najeriya.

Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa ya ce dakarun sojoji sun samu sababbin makamai, za su tunkari matsalar tsaro har sai sun ga bayanta.

Ya bayyana cewa matsin lambar da aka yi wa ’yan ta’adda a yankin Sahel ne ke kara tilasta musu kai hare-hare a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262