Ta Fara Tsami Tsakaninsu, Amurka Ta Zargi Isra’ila da Leken Asiri kan Jami’anta
- Wasu rahotanni sun fara jawo cewa an fara samun sabani tsakanin Amurka da Isra'ila yayin da ake ci gaba da yaki a Gabas ta Tsakiya
- Majiyoyi sun bayyana cewa Pentagon ta ɗaga matakin sa ido kan Isra’ila zuwa mafi girma saboda zargin tattara bayanan jami’anta
- An ce hukumomin leƙen asirin Amurka na fargabar Isra’ila na neman bayanai kan yadda gwamnatin Trump ke tattauna rikice-rikicen Gabas ta Tsakiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Wshington DC, US - Rahotanni sun bayyana cewa Pentagon ta ɗaga matakin tantance barazanar leƙen asiri daga Israel zuwa mafi girma.
Majiyoyi sun bayyana cewa hakan na da nasaba da zargin kan wasu ayyukan tattara bayanai daga Isra'ila kan jami'an gwamnatin Amurka.

Source: Getty Images
Zargin da Amurka ke yi wa Isra'ila
A cewar rahoton da NBC News ta wallafa, Hukumar Leken Asirin Tsaro ta Amurka (DIA) ta sauya matsayin Isra’ila zuwa mataki mai girma saboda ƙarin damuwa kan ayyukan leƙen asiri.
Rahoton ya ce wannan mataki ya biyo bayan zargin cewa jami’an leƙen asirin Isra’ila sun ƙara ƙoƙarin tattara bayanai daga manyan jami’an gwamnatin Amurka.
Wasu jami’an Amurka na yanzu da na baya sun bayyana cewa an fitar da wannan rahoto ne cikin makwannin baya saboda damuwa a tsakanin hukumomin leƙen asirin ƙasar.
A cewarsu, akwai fargabar cewa Isra’ila na son sanin bayanan tattaunawar cikin gida ta gwamnatin Donald Trump kan rikice-rikicen da ke gudana a Gabas ta Tsakiya.
Rahoton ya ƙara da cewa takardar tantancewar DIA mai shafuka bakwai ta kunshi wasu abubuwan da suka sa hukumar ta ƙara nuna damuwa.
Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da ake samun rahotannin sabani tsakanin Shugaba Trump da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu kan yaƙin Iran da kuma hare-haren sojin Isra’ila a Lebanon.
An kuma ruwaito cewa shugabannin biyu sun yi wata tattaunawa mai zafi ta wayar tarho a farkon wannan mako kan wasu batutuwan tsaro.

Source: Getty Images
Abin da ake zargin Isra'ila ke shirin aikatawa
Jami’an Amurka da masana harkokin tsaro sun ce Isra’ila na son fahimtar ko gwamnatin Trump za ta sake komawa manyan hare-haren soja kan Iran ko kuma ta zaɓi hanyar sulhu.

Kara karanta wannan
Isra'ila ta yi ikirarin hallaka kwamandan Hezbollah ana kokarin tsagaita wuta a Lebanon
Sai dai Jakadancin Isra’ila da ke Washington ya yi watsi da rahoton gaba ɗaya, yana mai cewa ƙarya ce cewa Isra’ila na leƙen asirin jami’an gwamnatin Amurka, cewar Tribune.
Haka kuma Pentagon ta ƙi yin tsokaci kan rahoton, yayin da wani jami’in Fadar White House ya musanta zarge-zargen tare da bayyana labarin a matsayin marar tushe.
Yadda Trump ya taimaki Isra'ila
Kun ji cewa shugaban Amurka Donald Trump ya yi karin haske game da jita-jitar cewa Benjamin Netanyahu ne ya cusa shi a yaki da Iran.
Trump ya musanta zargin da ake yada wa game da yaki da Iran inda ya bayyana cewa shi ne ya fara daukar matakin.
Ya kuma tabbatar da cewa ya yi magana mai zafi da Netanyahu saboda rashin jin dadinsa kan ci gaba da rikicin Isra'ila da Lebanon.
Asali: Legit.ng
