Tinubu Ya Fadi Manyan Kiristocin Najeriya da zai Tafi da Su Bikin Nada Sabon Fafaroma
- Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zai bar Abuja zuwa Roma, babban birnin kasar Italiya, domin halartar bikin nadin sabon Paparoma, Leo XIV
- Pope Leo XIV ya bukaci shugaban kasar da ya halarci wannan taro da ya ce yana da matukar muhimmanci ga cocin Katolika da duniya baki daya
- Bola Ahmed Tinubu zai halarci taron ne tare da manyan shugabannin darikar Katolika daga Najeriya, ciki har da Mathew Kukah da Lucius Ugorji
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai tashi daga Abuja zuwa birnin Roma a ranar Asabar domin halartar bikin nadin sabon Paparoma na cocin Katolika, Leo XIV.
Rahotanni sun bayyana cewa shugaba Bola Tinubu zai dawo Najeriya da zarar an kammala bikin a kasar Italiya.

Asali: Twitter
Fadar shugaban kasa ta wallafa a X cewa an gayyaci shugaban kasar Najeriya ne ta bakin Pietro Parolin, a madadin sabon Fafaroma Leo XIV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sabon Fafaroman ya bukaci ganin Tinubu a wajen taron da ya ce yana da matukar muhimmanci ga duniya.
Fafaroma Leo ya bayyana cewa Najeriya na da kima a wajensa domin ya taba aiki a ofishin jakadancin Vatican da ke Legas a shekarun baya.
Yaushe za a yi bikin nada sabon Fafaroma?
Za a gudanar da bikin nadin sabon Paparoma Leo XIV a ranar Lahadi 18 ga Mayu a dandalin St. Peter's da ke birnin Vatican.
Sabon Fafaroman da a baya ake kira da Robert Francis Prevost ya zama na 267 da ya hau wannan mukami.
An zabi Fafaroma Leo XIV ne kwanaki kadan bayan rasuwar tsohon Fafaroma Francis a ranar 21 ga Afrilu bayan zaman taron Cardinals da aka kada kuri'a.
Bola Tinubu zai tafi bikin nada sabon Fafaroma
Shugaba Tinubu zai tafi Roma tare da wasu muhimman mutane, ciki har da Ministan Harkokin Waje, Bianca Odumegwu-Ojukwu.
Sauran sun hada da Lucius Ugorji daga jihar Imo wanda shi ke shugabantar kungiyar Bishof-Bishof na Katolika ta Najeriya.

Asali: Facebook
Ignatius Kaigama na Abuja da Alfred Martins na Legas, da kuma Bishof Mathew Hassan Kukah na Sokoto, duk suna cikin tawagar shugaban kasar da za su halarci wannan biki mai tarihi.
Tinubu zai dawo gida bayan nadin Fafaroma
Ana sa ran shugaban kasa Bola Tinubu zai dawo gida Najeriya a ranar Talata, 20 ga Mayu, bayan kammala taron da ake ganin zai hada shugabanni daga fadin duniya.
Jaridar Punch ta wallafa cewa sanarwar ta fito daga Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabarun sadarwa, a ranar Laraba 15 ga Mayu, 2025.
Fa'idar ziyarar Tinubu
Ziyarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zuwa Vatican domin halartar bikin nadin sabon Fafaroma Leo XIV ba kawai ziyara ce ta addini ba, tana dauke da girman diplomasiyya da tasirin siyasa ga Najeriya.
A matsayinsa na shugaban kasa, kasancewar Tinubu a wannan muhimmin taro na nuna yadda Najeriya ke daukar dangantaka da kasashen duniya da muhimmanci.
Najeriya tana daya daga cikin manyan kasashen Afirka da ke da yawan mabiya addinin Katolika, kuma Vatican tana da ofishi na diflomasiyya a Legas.
Wannan ziyarar na iya kara dankon zumunci tsakanin Najeriya da Vatican, musamman wajen hadin gwiwa kan al’amuran zaman lafiya, yaki da talauci, da kuma sauyin yanayi.
Bugu da kari, kasancewar Tinubu a wajen nadin sabon Fafaroma na iya bude sabbin kofofi na fahimtar juna da kuma hada kai a matakin kasa da kasa.
A yayin da duniya ke fuskantar kalubale da dama, irin wannan ziyara na zama wata hanya ta bayyana matsayin Najeriya a kan teburin manyan kasashe masu fada a ji, tare da karfafa matsayin shugaban kasar a idon duniya.
Za a nuna ayyukan Tinubu a London
A wani rahoton, kun ji cewa ministocin shugaban kasa Bola Tinubu za su tafi birnin London domin nunawa duniya muhimman ayyukan da ya yi bayan hawa mulki.
Rahotanni sun bayyana cewa za a yi taron ne a London domin kowa ya fahimci irin kokarin da Bola Tinubu ya yi a kasa da shekara biyu.
Legit ta rahoto cewa daga cikin manyan jami'an gwamnatin Tinubu da za su halarci taron baje kolin ayyukan akwai ministan Abuja, Nyesom Wike.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng