An Yi wa Malamin Musulunci Kisan Gilla a Kwara, Ana Zaman Dar Dar a Yankin
- Al’ummar Musulmi sun shiga cikin tashin hankali bayan kashe fitaccen malamin addinin Musulunci a Kwara
- Dan majalisar Okuta/Yashikira, Muhammed Baba Saliu, ya ce har yanzu ana tattara bayanai kan lamarin
- Sarkin Fulanin Ilesha-Baruba a Kwara ya ce tarzomar da ta biyo baya ta shafi mutanen da ba su da alaka da kisan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ilorin, Kwara - Wani fitaccen malamin addinin Musulunci mai suna Alfa Iliyasu ya rasa ransa bayan an sare shi har lahira.
Lamarin ya faru ne a garin Ilesha-Baruba da ke karamar hukumar Baruten da ke jihar Kwara.

Source: Original
Shugabannin al’umma sun tabbatar da cewa malamin, wanda ake matukar girmamawa a Baruten da kewaye, an kashe shi ne a wani yanayi mai cike da ce-ce-ku-ce, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan
Kwankwaso ya san matsayinsa da Peter Obi ya ayyana abokin takararsa na zaben 2027
Abin da ɗan majalisar yankin ya ce
Dan majalisar dokokin Kwara mai wakiltar mazabar Okuta/Yashikira, Muhammed Baba Saliu, ya ce har yanzu al’umma na kokarin gano cikakkun bayanai kan lamarin.
Ya ce abin da suka sani shi ne an kashe malamin kuma an binne shi, yayin da ake samun rahotanni daban-daban kan wadanda ake zargi.
Tsohon shugaban karamar hukumar Baruten, Abdulrasheed Ibrahim, ya ce bayanan farko sun nuna cewa harin ya faru ne da misalin karfe 9:00 na safe.
A cewarsa, an kai malamin asibiti bayan harin, amma daga bisani ya mutu sakamakon munanan raunukan da ya samu a jikinsa.
Ibrahim ya kara da cewa an kama wanda ake zargi tare da kai shi hannun ’yan sanda kafin lamarin ya rikide zuwa tarzoma, cewar Sahara Reporters.

Source: Facebook
Sarkin yankin ya bayyana yadda lamarin ya ke
Sarkin Ilesha-Baruba, Alhaji Halidu Abubakar, ya tabbatar da aukuwar lamarin, yana mai cewa shugabannin gargajiya da na addini sun yi kokarin kwantar da hankali.
Ya ce wani mutum ya je ya kashe fitaccen malamin addinin Musulunci, Alfa Iliyasu, da adda, amma ba a san hakikanin abin da ya faru tsakaninsu ba.
Sai dai Sarkin Fulanin Ilesha-Baruba, Ardo Muhammed Abdullahi, ya yi zargin cewa tashin hankalin ya shafi mutanen da ba su da alaka da harin.
Ya ce wanda ake zargi mai suna Seke, wanda aka fi sani da Boso, ma’aikacin kwadago ne da aka sani a yankin kuma ya taba samun sabani kan albashi.
A cewarsa, mutumin ya shiga gidan malamin ne ya kai masa hari kafin ya yi kokarin tserewa daga wurin da abin ya faru.
Ya kara da cewa mazauna yankin sun kama wanda ake zargin tare da kai shi ofishin ’yan sanda kafin wasu fusatattun mutane su fitar da shi.
Abdullahi ya yi ikirarin cewa daga baya an kona gidaje da dama, ciki har da nasa guda uku, yayin da iyalansa suka tsallake rijiya da baya.
Ya ce har yanzu ba a gano inda ’ya’yansa biyu suke ba, kuma bai san ko suna raye ko sun mutu ba.
Kwara: Allah ya yi wa malamin Musulunci rasuwa
A wani labarin, an ji cewa an yi babban rashi a jihar Kwara bayan wani babban malamin addinin Musulunci ya yi bankwana da duniya a karshen shekarar Musuluncin bana.
Khalifatul-Adabiyah, Ash-Sheikh Abdulqodir Muhammad Kamaludeen Al-Adabiy ya yi bankwana da duniya a ranar Juma'a, 29 ga watan Mayun 2026.
Marigayin ya kasance kasance ɗa ga marigayi Sheikh Muhammad Kamaldeen Al-Adaby, wanda shi ne ya kafa gidauniyar Ansarul Islam Society of Nigeria.
Asali: Legit.ng

