Majalisa Ta Waiwayi 'Yan Najeriya, Za Ta Tilastawa Jama'a Kada Kuri'a a Lokutan Zabe

Majalisa Ta Waiwayi 'Yan Najeriya, Za Ta Tilastawa Jama'a Kada Kuri'a a Lokutan Zabe

  • Majalisar wakilai ta amince da kudirin tilasta wa 'yan Najeriya kada kuri’a a matakin karatu na biyu bayan tattaunawa a zauren majalisa
  • 'Dan majalisa Daniel Ago ya ce kudirin na da nufin sauya dokar zabe ta 2022 domin rage karancin fitowar jama’a zabe da kuma dakile sayen kuri’u
  • Sai dai wasu ‘yan majalisa kamar Mark Esset sun nuna adawa da kudirin, suna masu cewa kamata ya yi a fara gyara tsarin gudanar da zaben kasa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Wani kudiri da ke neman tilasta wa 'yan Najeriya da suka cancanta su kada kuri'a a lokacin zaɓe ya tsallake karatu na biyu a gaban majalisar wakilai.

Kudirin wanda Kakakin Majalisa, Tajudeen Abbas, ya gabatar, ya samu amincewar majalisa a matakin karatu na biyu bayan tattaunawa da aka yi a ranar Alhamis.

Majalisa
Majalisa za ta tilastawa yan Najeriya kada kuri'a Hoto: House of Representatives
Asali: Facebook

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa yayin jagorantar tattaunawar, Daniel Ago, wanda shi ma dan majalisa ne kuma mai daukar nauyin kudirin, ya ce za a sauya dokar zaben 2022.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa wannan zai bayar da damar rage karancin fitowa zabe da wasu daga cikin yan Najeriya ke yi idan an zo kada kuri'a.

Dalilin bijiro da kudirin tilasta zabe a Majalisa

Jaridar Vanguard News ta ce Hon. Ago ya bayyana cewa dokar tilasta yin zabe za ta karfafa wa jama'a su shiga harkokin siyasa ta hanyar sanya kada kuri’a.

Haka kuma za a wajabta wa jama'a kada kuri'a, a maimakon a ce mutum zai bi ra'ayinsa ne kawai wajen zuwa rumfunan zabe.

Majalisa
Tajudeen Abbas ne ya bijiro da kudirin tilastawa yan Najeriya gudanar da zabe Hoto: Abbas Tajudeen
Asali: Twitter

Ago ya kara da cewa idan aka amince da kudirin ya zama doka, hakan zai kara karfin dimokuradiyya ta hanyar samun wakilci na gaskiya, bunkasa wayar da kai ta siyasa da kuma rage sayen kuri’u.

Mataimakin Kakakin Majalisa, Benjamin Kalu, ya goyi bayan kudirin, tare da ambato kasar Ostiraliya inda yin zabe ya zama dole a doka.

Ya ce:

“A Ostiraliya, laifi ne rashin kada kuri’a a kowane zabe. Akwai wasu abubuwa da za a hana ka idan ba ka kada kuri’a ba."

Majalisa: An fafata kan kudirin tilasta zabe

Sai dai wani dan majalisa daga Akwa Ibom, Mark Esset, ya nuna adawa da kudirin, inda ya ce bai kamata majalisa ta tilasta wa mutane kada kuri’a ba alhali suna da rashin kwarin gwiwa kan tsarin zabe.

Ya ce:

“Kudiri ne mai kyau, amma kamar muna kokarin gini ne a kan iska. Duk da muna son a tilasta kada kuri’a, ya kamata a fara da yin dokar da za ta tabbatar da cewa kuri’un mutane na da amfani."

Lokacin da Kakakin majalisa ya nemi jin ra’ayin mambobin majalisa ta hanyar kuri’ar murya, masu goyon bayan sun fi masu adawa da kudirin.

Yan Najeriya sun yi martani ga kudirin majalisa

Wasu daga cikin yan kasa na ganin babu wanda zai tilasta masu gudanar da zabe saboda dalilai daban-daban.

Wata Ramlat ta shaidawa Legit cewa:

"Ina da katin zabe, amma ba zan yi zaben ba. Idan ma ka zaba, kana ji za a ba wani."

Wasu na ganin baya ga haka, ana cin zarafin mutane idan sun je kada kuri'a, musamman idan siyasa ta yi zafi.

Wata da ta nemi a sakaye sunanta ta ce:

Da mu ka je aikin zabe, wasu kamar yan Daba suka rika zaginmu da.masu zaben, suna cewa ai ba babanmu za a zaba ba." Saboda haka ko me za a yi Ni ba zan je zabe ba."

'Yan majalisar NNPP sun sauya sheka

A baya, mun wallfa cewa Majalisar wakilai ta tabbatar da sauya shekar wasu 'yan majalisa guda biyu daga jam’iyyar NNPP zuwa APC a zaman majalisar da aka gudanar a ranar Alhamis.

Kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ne ya karanta wasikun sauya shekar na ‘yan majalisar, Abdullahi Sani Rogo da Kabiru Usman Alhasan Rurum a gaban ‘yan majalisar.

'Yan majalisar sun danganta matakin sauya shekar da rikicin cikin gida da ya dabaibaye NNPP, lamarin da ke kara bayyana yadda jam’iyyar ke fama da rikice-rikice musamman a Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.