Sojoji da 'Yan Ta'adda Sun Gwabza Kazamin Fada a Kogi, An Rasa Rayuka

Sojoji da 'Yan Ta'adda Sun Gwabza Kazamin Fada a Kogi, An Rasa Rayuka

  • Dakarun rundunar sojin Najeriya ta 12 Brigade sun dakile wani shirin garkuwa da mutane tare da kashe dan ta’adda a jihar Kogi
  • Sojojin sun kai samame ne bayan samun sahihan bayanan sirri kan yunkurin ‘yan ta’addan na kai hari a yankin Jakura II
  • An kwato bindigar AK-47, harsasai 70, mujallu biyar da sauran kayayyakin da ake zargin ana amfani da su wajen aikata laifuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kogi - Dakarun rundunar sojin Najeriya ta 12 Brigade karkashin rundunar 2 Division sun samu nasarar dakile wani shirin garkuwa da mutane tare da kashe wani dan ta’adda a karamar hukumar Lokoja da ke jihar Kogi.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mukaddashin Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na rundunar soji, Laftanar Hassan Abdullahi, ya fitar a safiyar Lahadi.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun sace tsohon manjo janar da matarsa a Katsina

Dakarun sojoji da 'yan ta'adda sun gwabza fada a Kogi
Motar sojoji dauke da dakaru da ke aikin kakkabe 'yan ta'adda a Najeriya. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Sojoji sun fafata da 'yan ta'adda a Kogi

A cewar sanarwar, an gudanar da aikin ne a ranar 30 ga Mayun 2026 bayan samun sahihan bayanan sirri da suka nuna cewa wasu ‘yan ta’adda na shirin kai hare-haren satar mutane a yankin Jakura II, in ji rahoton Punch.

Laftanar Abdullahi ya bayyana cewa bayan samun bayanan sirrin, sojojin sun yi gaggawar tura dakaru zuwa wani wuri da ake zargin ‘yan ta’addan ke bi domin gudanar da ayyukansu.

“Bayan samun bayanan sirrin, dakaru sun mamaye wata hanyar da ake zargin ‘yan ta’addan ke amfani da ita a kan titin Old Obajana–Tajimi, inda suka shirya kwanton bauna domin hana su aiwatar da shirinsu,” in ji shi.

Ya ce bayan ‘yan ta’addan sun iso wurin, sai aka yi musayar wuta mai tsanani tsakanin bangarorin biyu.

An kashe dan ta’adda guda

A yayin artabun, sojojin sun samu nasarar kashe daya daga cikin ‘yan ta’addan, yayin da sauran suka tsere zuwa cikin daji dauke da raunukan harbin bindiga.

Kara karanta wannan

Mai dokar barci: Sojoji sun damke 'dan bijilanti da zargin yi wa ISWAP leken asiri

Bayan kammala farmakin, sojojin sun ci gaba da bincike a yankin inda suka gano wasu makamai da kayayyaki da ake zargin mallakin ‘yan ta’addan ne.

Kayayyakin da aka kwato sun hada da bindiga kirar AK-47 guda daya, mujallu biyar, harsasai 70 na musamman masu girman milimita 7.62, bandoliyar harsasai guda daya da kuma wayoyin hannu.

A cewar rundunar, kayayyakin da aka kwato sun kara tabbatar da cewa kungiyar na da hannu a ayyukan garkuwa da mutane da sauran laifuka a yankin, in ji rahoton The Nation.

'Yan bindiga sun yi yunkurin sace mutane a Kogi amma sun gamu da fushin sojoji
Taswirar jihar Kogi da ke a Arewa ta Tsakiya. Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ana ci gaba da farautar wadanda suka tsere

Laftanar Abdullahi ya ce dakarun sojin na ci gaba da gudanar da bincike da sintiri a yankin domin gano inda sauran ‘yan ta’addan da suka tsere suka buya.

Ya kara da cewa rundunar ba za ta sassauta ba wajen matsa wa masu aikata laifuka lamba har sai an kawar da su gaba daya.

Kwamandan rundunar 12 Brigade, Birgediya Janar Kasim Umar Sidi, ya yabawa dakarun bisa jajircewa, kwarewa da sadaukarwar da suka nuna yayin aikin.

'Yan ta'adda sun firgita a Kogi

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi wa Boko Haram ruwan bama bamai ana shirin sallah

A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnatin Kogi ta ce matsin lamba da ruwan wuta daga jami’an tsaro ya tilasta wa wasu ’yan bindiga neman sulhu da mika makamansu.

Mai bai wa gwamna shawara kan tsaro ya ce amfani da fasaha da kayan aiki ya raunana ’yan ta’adda sosai.

Gwamnati ta jaddada matsayarta game da tattaunawa da ’yan bindiga ba, tana shirin kafa doka da za ta haramta zama a daji a fadin jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com