2027: Mace Ta Zama Yar Takarar Shugabar Kasa a YPP, Za Ta Kara da Su Tinubu, Obi

2027: Mace Ta Zama Yar Takarar Shugabar Kasa a YPP, Za Ta Kara da Su Tinubu, Obi

  • Jam’iyyar YPP ta amince da Anita Zugwai-Chukwu a matsayin ‘yar takarar shugaban kasa daya tilo domin wakiltarta a zaben 2027
  • Anita Zugwai-Chukwu ta yi alkawarin fifita muradun 'yan Najeriya, tare da tabbatar da manufofin jam’iyyar idan ta lashe zaben mai zuwa
  • Shugaban YPP, Bishop Amakiri, ya kaddamar da shirin “Agenda 469” domin karfafa tasirin jam’iyyar a Majalisar Dokoki ta Kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Jam’iyyar YPP ta amince da shugabar matanta ta kasa, Anita Zugwai-Chukwu, a matsayin ‘yar takarar shugaban kasa a babban zaben shekarar 2027.

An tabbatar da Zugwai-Chukwu ne a matsayin ‘yar takara daya tilo a yayin babban taron kasa na uku na jam’iyyar da aka gudanar a Abuja ranar Asabar.

Jam'iyyar YPP ta tsayar da mace a matsayin 'yar takararta ta shugaban kasa a 2027
Mrs Anita Zugwai-Chukwu wadda ta zama 'yar takarar shugabar kasa a YPP. Hoto: Young Progressives Party
Source: Facebook

Shugabannin jam’iyyar sun bayyana matakin a matsayin wani muhimmin yunkuri na sake tsara jam’iyyar domin tunkarar babban zaben da ke tafe.

Kara karanta wannan

NNPP ta hakura da tsayar da dan takarar shugaban kasa a 2027, ta bayyana dalili

Taron ya samu halartar manyan jami’an jam’iyyar na kasa, shugabannin jihohi da wakilai daga sassan Najeriya daban-daban.

Anita ta gode wa shugabannin YPP

A jawabin karbar tikitin takara, Zugwai-Chukwu ta nuna godiyarta ga shugabannin jam’iyyar bisa amincewar da suka nuna mata.

“Da farko ina mika godiyata ga shugaban jam’iyya na kasa, mambobin kwamitin zartarwa na kasa da shugabannin jihohi saboda jajircewarsu, hikimarsu da shugabanci nagari. Kokarinku ne ya sa wannan rana ta tabbata. YPP tana da karfi ne saboda ku masu karfi ne,” in ji Anita.

Ta ce tana sane da irin kalubalen da ke gaban Najeriya da kuma jam’iyyar, tana mai jaddada cewa ‘yan Najeriya na neman shugabanci mai gaskiya da rikon amana.

‘Yan Najeriya na neman shugabanci nagari

Zugwai-Chukwu ta ce al’umma sun gaji da matsalolin da suke fuskanta, kuma suna bukatar shugabanni da za su sanya muradun jama’a gaba.

A cewarsa:

“Ina da masaniya kan kalubalen da ke gabanmu a matsayin kasa da kuma jam’iyya. ‘Yan Najeriya na bukatar shugabanci mai gaskiya kuma mai kula da damuwar jama’a."

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Atiku ya girma, ya samu tikitin takarar shugaban kasa a zaben 2027

Ta kuma yi alkawarin cewa idan aka zabe ta matsayin shugaban kasa, za ta mayar da hankali wajen kare manufofin jam’iyyar da aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki.

“A matsayina na ‘yar takarar shugaban kasa, aikina a bayyane yake. Zan kare hangen nesan jam’iyyarmu, in mutunta kundin tsarin mulki tare da yin aiki kafada da kafada da masu ruwa da tsaki da kuma kwamitin gudanarwa na kasa. Burina na kaina ba zai zama a gaba ba,” in ji Anita.
YPP ta kaddamar da wani shiri na mamaye majalisar tarayya a 2027.
Tambarin jam'iyyar YPP da ta tsayar da mace matsayin 'yar takarar shugabar kasa a 2027. Hoto: Young Progressives Party
Source: Facebook

YPP ta kaddamar da Agenda 469

Tun da farko, shugaban jam’iyyar na kasa, Bishop Amakiri, ya bayyana sabon tsarin siyasar da jam’iyyar za ta bi gabanin zaben 2027.

Ya ce jam’iyyar ta kaddamar da wani sabon tsari mai suna “Agenda 469”, wanda aka tsara domin kawo sauyi a siyasar Najeriya.

Shugaban jam’iyyar ya bayyana cewa manufar shirin ita ce karfafa tasirin YPP a Majalisar Dokoki ta Kasa domin samar da dokokin da za su amfani talakawan Najeriya.

An kori dan majalisa daga YPP

A wani labari, mun ruwaito cewa, jam'iyyar YPP ta bayyana cewa ta samu bidiyo da ke tabbatar da zargin da ake wa dan majalisar wakilai, Hon Uzokwe Peter na cin amana.

Kara karanta wannan

Duk da rikicin PDP, tsagin Turaki ya ba Jonathan tikitin takarar shugaban kasa

A taron kwamitin zartarwa (NEC) na YPP ta kasa, jam'iyyar ta yanke shawarar korar dan Majalisar tarayyar bisa zarge-zargen da ke kansa.

Haka nan kuma jam'iyyar YPP ta yi fatali da duk wani yunkuri na maida Najeriya kasa mai bin tsarin jam'iyya daya, ta ce hakan barazana ce ga dimokuradiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com