An Shiga Jimami da Tsohon Direban Jirgin Saman Shugaban Kasa Ya Rasu a Kaduna

An Shiga Jimami da Tsohon Direban Jirgin Saman Shugaban Kasa Ya Rasu a Kaduna

  • Tsohon hadimin shugabannin ƙasa, Kyaftin Shehu Iyal ya rasu a ranar Alhamis bayan fama da jinya, a cewar iyalansa
  • Marigayin ya taba zama mataimaki na musamman a zamanin Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan, sannan ya shugabanci kamfanin Afri Air
  • Za a yi jana’izarsa yau Juma’a da yamma a unguwar Ƙwarbai da ke cikin birinin Zaria, kamar yadda iyalansa suka tabbatar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Zaria, Kaduna - Al'ummar jihar Kaduna sun yi babban rashi bayan sanar da rasuwar dattijo wanda ke taimakon al'umma.

An tabbatar da rasuwar tsohon matukin jirgin saman shugaban kasa, Kyaftin Shehu Iyal bayan ya sha fama da jinya.

An yi rashin tsohon hadimin shugaban kasa
Tsohon hadimin shugaban kasa ya rasu. Hoto: Eminence Royalty Magazine.
Asali: Facebook

Ƙwararren matuƙin jirgin sama ya rasu a Kaduna

Rahoton Aminiya ya ce marigayin wanda ya rike muƙamin hadimin tsohon shugaban kasa ya rasu a ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Marigayin ya taba rike mukamin mataimaki na musamman kan harkokin jiragen sama a zamanin Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan.

Kafin rasuwarsa, shi ne shugaban kamfanin jiragen sama mai suna Afri Air, kuma jigo ne a fannin sufurin jirage a Najeriya.

A shekarar 1977, ya kammala digirinsa a Jami’ar Ahmadu Bello, sannan ya wuce Kwalejin Koyon Tuƙin Jiragen Sama (NCAT) da ke Zaria.

Ya rike mukamai daban-daban a bangaren sufurin jirage, ciki har da kula da sashen zirga-zirga na Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa.

An bayyana Shehu Iyal a matsayin gwarzon jinƙai da ya shahara wajen taimakon al’umma, rayuwarsa ta shafi ɗumbin mutane.

Kaduna ta yi rashin dattijo kuma mai taimakon al'umma
An sanar da rasuwar tsohon hadimin shugaban kasa a Kaduna. Hoto: Legit.
Asali: Original

An fadi gudunmawar marigayin a Kaduna

Tarihi da abubuwan da ya bari za su kasance cikin zukatan waɗanda ya tallafa wa da dangoginsu da ya ɗaga.

An ce mutum ne mai tsananin ƙaunar addini, inda soyayyarsa ga Musulunci ta kasance abin koyi.

A jihar Kaduna, sunansa ya ratsa kowane gida saboda tsayuwarsa kan biyayya da sadaukarwa.

Marigayi Iyal ya kasance babban jigo a harkar jiragen sama a Najeriya, inda ya bar tarihin da ba za a manta da shi ba.

A matsayinsa na Babban Mashawarci na Musamman kan harkar jiragen sama ga tsoffin shugabanni biyu, Obasanjo da Jonathan ya bayar da gudunmawar fasaha da hangen nesa wajen tsara makomar harkar a ƙasa.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an shirya gudanar da sallar jana'izar marigayin a yau Juma'a a unguwar Kwarbai da ke Zaria.

“Za a yi jana’izar Kyaftin Shehu Iyal a yau Juma’a da yamma a unguwar Ƙwarbai cikin birnin Zaria."

- Cewar danginsa

Mahaifin tsohon gwamnan Kaduna ya kwanta dama

Kun ji cewa Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai da ƴan uwan marigayi Alhaji Ramalan Yero wanda ya bayyana a matsayin dattijon arziki.

An sanar da rasuwar Turakin Dawakin Zazzau wanda ya kasance mahaifin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero.

Uba Sani ya ce marigayin mutum ne mai addini wanda ya taimaki al'umma, yana mai cewa masarautar Zazzau ta yi babban rashi da zai yi wahalar cike gibinsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.