Abin da Sultan Ya Yi da Shehi Ya Buƙaci Obasanjo Ya Bar Kiristanci Zuwa Musulunci
- Sheikh Sulaiman Onikijipa ya bukaci tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya karɓi Musulunci saboda irin gudummawar da ya bayar a addinin
- An bayyana wannan kira yayin gabatar da sabon tsarin sake fasalin babban masallacin Egba da ke Abeokuta a ranar Juma'a 18 ga watan Afrilun 2025
- A cikin bidiyon da ke yawo, an ga Sultan na Sokoto yana kada kai alamar yarda da kira ga Obasanjo da kuma nuna shi da yatsa
- Malamin ya ce ya kamata Obasanjo ya yi shahada domin fara salla saboda samun ladan aikin da ya yi da yake addinin kirista
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Egba, Abeokuta, Ogun - Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya samu kira da ya bar Kiristanci ya rungumi Musulunci.
Malamin Musulunci, Sheikh Sulaiman Faruq Onikijipa shi ya yi kiran saboda gudummawar da Obasanjo ya bayar ga addinin Musulunci.

Asali: Twitter
Hakan na cikin wani faifan bidiyon YouTube wanda shafin MTC ya wallafa a manhajar a jiya Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin Musulunci ya roƙi Obasanjo ya bar Kiristanci
Sheikh Onikijipa wanda Babban Mufti ne na Ilorin ya yi wannan kiran a wajen gabatar da sabon tsarin masallacin Egba da ke Abeokuta.
Malamin a cikin yaren Yarbanci ya bukaci Obasanjo da ya karɓi Musulunci da yin salla kafin mutuwarsa domin samun sakamako daga Allah.
Wannan kira ya zo ne yayin da malamin ke wa’azi a bikin gabatar da zane-zanen sake fasalin masallacin Egba.
Bikin ya gudana ne a ranar Juma’a, 18 ga Afrilu, wanda ya zo daidai da ranar 'Good Friday' ta Kiristoci a wannan shekarar.

Asali: Facebook
Abin da Sultan ya yi kan kiran Obasanjo
A cikin bidiyon, an ga Sultan na Sokoto, Alhaji Muhammadu Abubakar III yana kada kai da nuna yarda da kiran da Onikijipa ya yi ga tsohon shugaban kasar.
Sultan na Sokoto, wanda ya halarci bikin, an gan shi yana kaɗa kai da nuna Obasanjo da yatsa yayin da Onikijipa ke magana.
Sheikh Onikijipa ya ce Obasanjo ya bayar da gudummawa ga Musulunci sosai, hanyar samun lada gaba ɗaya ita ce yin salla da shahada.
Malamin ya kara da cewa dole ne Obasanjo ya furta “Laillaha Illalah, Muhammadu Rasulullah” domin shaidar imani da cikakken shiga addinin Musulunci.
Ya ce Obasanjo ya gina babban masallacin kasa a Abuja kuma yanzu yana tallafa wa sake fasalin masallacin Egba da ke Abeokuta.
Sheikh Onikijipa ya kwatanta Obasanjo da wani sahabin Annabi (SAW) da bai zama Musulmi ba amma yana kula da Annabi har Annabi ya so ya Musulunta.
Sultan, Obasanjo sun roki taimakon gyaran masallaci
A wani labari, tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya bukaci 'yan Najeriya su rika yin ayyukan alheri domin samun lada daga Allah.
Obasanjo ya yi kiran ne yayin kaddamar da gyaran masallaci a garin Egba da ke birnin Abeokuta a jihar Ogun da ke Kudancin Najeriya.
Sarkin Musulmi da sauran manyan baki sun yaba da aikin, inda aka ce gidaje 78 za a rusa kuma a samar da sababbin matsuguni.
Asali: Legit.ng