An Bincika An Gano Dalilin Ganin Nasir El Rufa'i a Coci bayan Ƙorafin Jama'a
- Masu amfani da shafukan sada zumunta sun fahimci wani hoton tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i a baibai
- Wani Scroc Partner ya wallafa hotonsa da ke nuna alamar El-Rufa'i ya shiga coci, inda aka zarge shi da zuwa neman kuri'a
- Yadda jama'a suka dauki zafi a kan batun ya sa aka gudanar da binciken kwakwaf don sanin abin da ya kai El-Rufa'i coci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Masu amfani da shafukan sada zumunta sun yiwa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i rubdugu kan wani hotonsa da aka wallafa a ranar 3 ga Mayu, 2025.
Hoton, wanda ya nuno nuna tsohon Ministan Abuja, Nasir El-Rufai, yana tare da wasu mutane a wani taro da ya yi kama da na coci ya jawo hankalin jama'a sosai.

Asali: Twitter
Sroc Partner da ya wallafa hoton a Facebook ya rubuta cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"2027: Malam Nasir El-Rufai yanzu yana halartar taron cocin domin ya lallashi al’ummar Kirista da ya taba bayyana ra’ayi mai tsauri a kansu."
Jama’a sun yiwa El-Rufai rubdugu kan zuwa coci
The Nation ta wallafa cewa wasu ‘yan Najeriya sun bayyana ra’ayoyinsu kan abin da suka kira wata dabara ta yakin neman zaben Nasir El-Rufa'i.
Wani mai suna Lekan Awe, ya rubuta cewa:
"Wannan yaudara ce! A lokacin da yake gwamna yana gallaza wa Kiristoci. ‘Yan siyasar Najeriya ba za su mutu lafiya ba, Wallahi!"
Shi ma wani, Olalekan Quadri, ya ce:
"El-Rufai abinkunya ne ga yankinsa, ‘yan tsirarun Fulani masu hada kai domin sake karbe mulki don danne talakawan Najeriya. Ba zai yi nasara ba in sha Allah, Ameen."

Asali: Twitter
Wani mai amfani da Facebook, Ojo Victor Echo, shi ma ya wallafa wannan hoto a ranar 2 ga Mayu, 2025, tare da taken:
"Abin mamaki bai kare ba, tsohon gwamna Nasir El-Rufa'i yana cikin taron coci."
An yi bincike kan zuwan El-Rufai coci
Yadda wannan hoto ke yawo a kafafen sada zumunta ya sa shafin binciken kwakwaf na Dubawa ya gudanar da bincike domin tantance gaskiyar al’amarin.
An gano cewa Nasir El-Rufai da kansa ne ya wallafa hoton a shafinsa na X a ranar 1 ga Mayu, 2025.
A cikin rubutunsa, ya bayyana cewa ya halarci jana’izar Cif Mathias Chidi Anohu tare da iyalan Anohu a Okija da taken:
"Mun hadu da iyalan Anohu a jana’izar Chief Mathias Chidi Anohu da aka gudanar da safe a Okija.
Allah ya jikansa da rahama."
Meye ya kai El-Rufai coci?
Masu bibiyar labarai sun lura cewa hoton tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i, yana halartar wani taron cocin ya jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta.
Sai dai, ya zuwa yanzu ba a san meye ya kai El-Rufai cocin ba domin ba a fayyace ba a labarin farko, wanda hakan ke haifar da jita-jita da kuma rudani a tsakanin jama’a.
A bangare guda, rahotanni daga jaridar The Nation da Daily Trust sun nuna cewa El-Rufa’i ya halarci jana’izar Chief Mathias Chidi Anohu, wani mashahurin dan siyasa kuma babban dan jam’iyyar APC a yankin Kudu maso Gabas.
Wannan bayanin ya fito ne daga rubutun El-Rufa’i a shafinsa na X (tsohuwar Twitter) inda ya bayyana cewa ya halarci jana’izarsu a Okija, jihar Anambra.
Wannan bayani ya sa aka rage zargin cewa El-Rufa’i na amfani da wannan ziyara domin yakin neman zabe, domin ana ganin jana’iza ba wuri ne na siyasa kai tsaye ba.
Duk da haka, wasu ‘yan Najeriya na kallon wannan al’amari a matsayin wata dabarar siyasa musamman saboda lokacin da aka dauki hoton ya zo kusa da fara yakin neman zaben 2027.
Bwala: 'Farin jinin El-Rufa'i ya dusashe'
A baya, kun ji cewa hadimin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, Daniel Bwala, ya bayyana cewa siyasar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ta fuskanci koma baya.
Ya ce rashin karbuwa da jam’iyyar APC ta fuskanta a zabukan 2019 a Kaduna na nuna irin dushashewarsa, domin tun kafin ya bar mulki ya fara fuskantar matsala.
Bwala ya kuma yi tsokaci kan ra'ayin wasu daga yankin Kudu cewa bayan Arewa ta yi shekara takwas a mulki, ya kamata yanzu a bar dan yankinsu ya yi shekara takwas.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng