Abu Ya Kai Makura, Majalisa Ta Bukaci Cafke Ƴan Bindiga da ke Wasa da Kuɗi a TikTok
- Majalisar Dattawa ta umarci hukumomin tsaro su gano tare da cafke 'yan bindiga da 'yan ta'adda masu nuna kudade a TikTok
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta ce wasu 'yan bindiga sun raba sama da Naira miliyan 100 ta TikTok cikin mintuna 30
- Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya bukaci jami'an tsaro su dauki lamarin da muhimmanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Majalisar Dattawa ta umarci hukumomin tsaro su kawo karshen yan ta'adda a fadin Najeriya.
Majalisar ta bukaci su kara kaimi wajen gano, bibiya da cafke 'yan bindiga da 'yan ta'adda da ke nuna kudaden da suka samu ta kafafen sada zumunta.

Source: Facebook
An cimma wannan matsaya ne bayan Sanata Sunday Karimi, mai wakiltar Kogi ta Yamma, ya gabatar da kuduri kan karuwar hare-haren 'yan bindiga da 'yan ta'adda a yankinsa da sauran sassan Najeriya, cewar Tribune.

Kara karanta wannan
Majalisar Dattawa ta hana Katsina da wasu jihohin Najeriya yin sulhu da 'yan bindiga
Ta'addanci: Sanata Natasha shawarci hukumomin tsaro
Yayin muhawarar, Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta bukaci a kara da kira ga Cibiyar Yaki da Laifukan Yanar Gizo ta 'yan sanda da sauran hukumomi su bibiyi masu yada ayyukan ta'addanci.
Natasha ta nuna damuwa kan yadda kungiyoyin masu aikata laifuffuka ke kara nuna rashin tsoro, tana cewa wasu daga cikinsu suna nuna yadda suke gudanar da ayyukansu tare da baje kolin dukiyarsu a TikTok.
Ta ce:
"Yan ta'addan da ke aikata wadannan laifuffuka suna bayyana kai tsaye a shafukansu na sada zumunta, kwanaki biyu da suka gabata, sun yi rabon kudi sama da Naira miliyan 100 cikin mintuna 30 a TikTok."

Source: Twitter
Ayyukan yan bindiga ya fusata majalisa
Sanatar ta yi mamakin yadda hukumomin tsaro ba su kama mutanen da ake zargin suna aikata laifuffuka ba duk da kasancewarsu da bayyanannun shafukan sada zumunta da jama'a ke gani.
Ta kara da cewa:
"Ina mamakin dalilin da ya sa bangaren yaki da laifukan yanar gizo da rundunar 'yan sanda ba za su iya bibiyar wadannan ayyuka su kama masu aikata su ba. Don haka ina kira a cafke su."
Sanata Osita Ngwu mai wakiltar Enugu ta Yamma ya mara wa wannan bukata baya, yayin da mafi yawan sanatoci suka nuna cikakken goyon bayansu ga kudurin.
Da yake mayar da martani, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici da nuna rashin tsoron doka, yana kalubalantar hukumomin tsaro su dauki mataki.
Ya ce:
"Ya kamata Hukumar DSS ta iya bibiyar lamuransu tare da kama su domin wannan nuna isa ne, tamkar babu doka a kasar nan."
Akpabio ya ce bidiyoyin da ke yawo na masu aikata laifuffuka suna nuna kudade tare da tallata ayyukansu kamar kalubale ne ga gwamnati da hukumomin tsaro, cewar Punch.
Shugaban Majalisar ya bukaci shugabannin hukumomin tsaro su dauki wannan batu a matsayin babban kalubale tare da inganta hadin gwiwa wajen amfani da bayanan sirri daga intanet.
Dattawan Arewa sun ba da shawarar kawo tsaro
Mun ba ku labarin cewa kungiyar dattawan Arewa ta bukaci Shugaba Bola Tinubu ya yi gaggawar kawo karshen matsalar tsaro a kasar.
Dattawan sun bukaci ya ayyana dokar ta-baci kan tsaro, tana cewa Najeriya na fuskantar mummunar barazana.
NEF ta ce sace-sacen mutane, ta'addanci da hare-haren 'yan bindiga sun mamaye yankuna da dama, lamarin da ya jefa al'umma cikin tsoro.
Asali: Legit.ng
