Fatima Ta Yi Nasara, Kotu Ta Yanke Hukunci kan Hausawan da Aka Haifa a Jos ta Arewa
- Babbar Kotun Jihar Filato ta yanke hukuncin cewa duk wani Bahaushe da aka haifa kuma ya taso a Jos ta Arewa ɗan asalin yankin ne
- Kotu ta umarci ƙaramar hukumar Jos ta Arewa ta ba Fatima Baba Akawu takardar shaidar zama cikakkiyar 'yan asalin ƙasa
- Alƙalin kotun, Mai shari'a C. Donglong ya ce nuna bambanci saboda ƙabila ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jos, Nigeria - Babbar Kotun Jihar Filato mai lamba 17 ta yanke hukuncin cewa Hausawan da aka haifa kuma suka taso a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa 'yan asalin yankin ne.
Mai shari'a C. Donglong ne ya yanke hukuncin a ƙarar da Fatima Baba Akawu da mahaifinta, Baba Alhaji Akawu, suka shigar kan ƙin ba ta takardar shaidar yar asalin ƙasa daga ƙaramar hukuma.

Source: Getty Images
Dalilin shigar da ƙara a kotu
Daily Trust ta ce masu ƙarar sun nemi kotu ta fayyace ko Fatima Baba Akawu, wadda aka haifa a Jos ta Arewa kuma mahaifinta ɗan asalin yankin ne, tana da damar samun takardar shaida duk da kasancewarta Bahaushiya.
Sun kuma kalubalanci matakin ƙaramar hukumar na ba ta takardar zama maimakon takardar yar asalin yankin, yayin da aka ba wani mutum mai suna Dung Bot, ɗan ƙabilar Berom, takardar ɗan asalin ƙasa a rana guda.
Alƙali ya soki nuna bambanci
Da yake yanke hukunci, Mai shari'a Donglong ya amince da dukkan buƙatun masu ƙarar.
Ya bayyana cewa matakin da ƙaramar hukumar ta ɗauka na ba Fatima takardar zama saboda asalinta na Bahaushiya, amma ta ba wani ɗan Berom takardar ɗan asali, wani nau'i ne na nuna bambanci da ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya.
Alƙalin ya jaddada cewa kotu tana da alhakin kare haƙƙin kowane ɗan Najeriya daga wariya bisa ƙabila ko asalinsa.
Umarnin da kotu ta bayar
Kotu ta ayyana cewa saboda Baba Alhaji Akawu cikakken ɗan asalin Jos ta Arewa ne, dukkan 'ya'yansa da aka haifa kuma suka taso a yankin, ciki har da Fatima, suna da cikakkiyar damar a gane su a matsayin 'yan asalin karamar hukumar.

Source: Original
Har ila yau, kotun ta bayar da umarnin da ya hana ƙaramar hukumar Jos ta Arewa ci gaba da ba mutane takardar zama a matsayin madadin takardar ɗan asalin ƙasa.
Alƙalin ya bayyana cewa irin wannan takarda ba ta da tushe a doka kuma ba za ta iya maye gurbin takardar ɗan asalin ƙasa ba.
Kotu ta tura Halima Umar gidan yari
A wani labarin, kun ji cewa kotu ta yanke wa wata mata, Halima Umar hukuncin daurin shekaru 20 a gidan gyaran hali bisa mallakar tarin makamai ba bisa ka'ida ba.
Rahotanni sun nuna cewa an kama matar da laifin mallakar harsasai 302 na bindigar AK-47 ba bisa ka’ida ba da yunkurin bayar da tallafi wajen aikata ayyukan ta’addanci.
Hukumar tsaro ta DSS ta gurfanar da Halima Umar a gaban kotu ne a ranar 11 ga Maris, 2026 bayan kama ta da makamai da ake zargin za ta kai wa 'yan bindiga a jihar Filato.
Asali: Legit.ng

