Obasanjo, Atiku, Obi da Manyan Najeriya Sun Dura Abuja, An Fara Taron Sule Lamido

Obasanjo, Atiku, Obi da Manyan Najeriya Sun Dura Abuja, An Fara Taron Sule Lamido

  • Tsofaffin shugabannin Najeriya, mataimakansu da na shugabannin majalisar dattawa sun halarci ƙaddamar da littafin Sule Lamido a Abuja
  • An rahoto cewa tsohon shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu, ya yi bitar littafin tsohon gwamnan na Jigawa mai "Being True to Myself"
  • Obasanjo ya kira Sule Lamido da matsayin 'amintacce' kuma 'mai kishin Najeriya', wanda a cewarsa ya taka rawar gani a lokacin yana gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, tsofaffin mataimakan shugaban kasa, Atiku Abubakar da Namadi Sambo sun dura birnin tarayya Abuja.

Tsofaffin shugabannin majalisar dattawa, Ken Nnamani da Anyim Pius Anyim, suma sun isa Abuja, inda ake ƙaddamar da littafin tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido.  

Obasanjo, Atiku da jiga jigan Najeriya sun halarci bikin kaddamar da littafin Sule Lamido a Abuja
Atiku Abubakar (hagu), Sule Lamido (tsakiya) da Olusegun Oabsanjo (dama). Hoto: @atiku
Asali: Twitter

Kusoshin Najeriya sun dura a Abuja

Jaridar Punch ta rahoto cewa tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Iyorchia Ayu, zai yi bitar tarihin rayuwar Lamido mai taken 'Being True to Myself'.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin waɗanda suka halarci ƙaddamar da littafin da ke gudana a cibiyar taro ta NAF a Abuja, akwai ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi.

Rahoton ya kuma nuna cewa gwamnan Gombe, Muhammadu Yahaya da takwarorinsa na Jigawa, Umar Namadi; da Plateau, Caleb Mutfwang sun halarta.

Haka nan akwai fitattun mutane da yawa da suka halarta, ciki har da tsofaffin gwamnoni, Gabriel Suswam (Benue), Ahmed Makarfi (Kaduna), Babangida Aliyu (Niger), Liyel Imoke (Cross Rivers) da sauransu.

Abin da Obasanjo ya ce kan Sule Lamido

Jaridar Tribune ta rahoto cewa Obasanjo ya halarci taron ne a matsayin babban bako na musamman, wanda hakan ya nuna irin ƙawancen da ke tsakaninsa da Lamido, wanda ya naɗa ministan harkokin waje a 1999.  

A yayin taron, Obasanjo ya kambama Sule Lamido, yana mai cewa:

"Sule yana da hali mai ban sha'awa, kuma amintacce ne. Muna da ra'ayi iri daya tun lokacin da muke cikin gwamnati. A lokacin da muka hau mulki, Najeriya ta kasance saniyar ware, mun yi damarar aiki tukuru a ciki da wajen kasar.
"Ya yi aiki mai ban mamaki (a matsayin ministan harkokin waje) wanda ya sa Sarauniyar Ingila da kungiyar Commonwealth suka zo Najeriya don CHOGM, wanda ya canja kallon da ake yi mana a Afirka da duniya.
"Sule yana da burin ci gaban Najeriya, kuma ya yi aiki tukuru a matsayin gwamna. Hakkin kowane ɗayanmu ne mu ga cewa mun mayar da Najeriya irin wadda muke mafarkin ta."
Obasanjo ya yi ruwan kalaman yabo ga Sule Lamido yayin kaddamar da littafin Lamido a Abuja
Tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido. Hoto: @SuleLamidoVgd
Asali: Twitter

Takaitaccen bayani game da littafin Sule Lamido

Jaridar The Sun ta ce littafin ya yi bayanin gwagwarmayar Sule Lamido tun daga Jamhuriya ta biyu, ta cikin PRP a ƙarƙashin Aminu Kano, zuwa rawar da ya taka a PDP a Jamhuriya ta huɗu.

Ya yi bayanin ci gaban siyasar Najeriya, tare da bayyana cikakkun bayanai game da ayyukan sojoji, gwagwarmayar dimokuraɗiyya, da makirce-makircen da suka shafi ƙasar a cikin shekaru da yawa, a mahangar Sule Lamido.

Sanata Mustapha Khabeeb, shugaban kwamitin taron, ya bayyana littafin a matsayin wani kundi mai bayyana tarihin Najeriya, cike da abubuwan mamaki, tashin hankali, da yaudara.

Shawarar da Obasanjo ya bayar a baya na maye gurbin Sambo da Sule Lamido a matsayin mataimakin takarar Jonathan a 2015 ya haifar da tashin hankali, wani bayanin tarihi da aka ji a wajen taron.

A lokuta da dama na biki ko taro, sau tari a kan samu haduwa tsakanin manyan 'yan siyasar kasar nan, ciki har da abokan hamayya da ke bin mazhabar jam'iyyu mabambanta.

A wannan karon ma ba ta sauya zane ba, duk da cewa akwai da dama da suka kasance a tafiya da shekarun ba.

A gefe guda, hakan na barin 'yan kasa da tofa albarkacin bakinsu kan yadda ake mayar da su saniyar ware a taruka irin wadannan.

'Makomar Najeriya idan PDP ta tarwatse' - Lamido

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya yi gargaɗi cewa yunƙurin raunana PDP na iya haifar da rugujewar tsarin dimokuraɗiyya a Najeriya.

Ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da amfani da hukumomin gwamnati, kamar su ‘yan sanda, wajen raunana jam’iyyun adawa a ƙasar.

Sule ya nuna damuwa game da yadda mambobin PDP ke ficewa zuwa APC, yana mai cewa waɗanda suka shiga APC saboda tsoro za su yi nadama daga baya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.