Albashi N500,000: ’Yan Kasar Sin Suka Shigo Najeriya, Sun Kafa Kamfanin Sarrafa Lithium a Nasarawa
- An kawo kamfanin sarrafa lithium a jihar Nasarawa, gwamna Abdullahi Sule ya fadi abin da ke ransa kan shigowar ‘yan Sin
- Gwamna y aba ‘yan jiharsa shawara mai kyau kan yadda za su samu ayyuka a kamfanin ‘yan kasar Sin don rike kansu
- Ana hakar ma’adinai a Najeriya, sai dai kusan ‘yan kasar karewa suke a matsayin leburori da ke aikin wahala a wuraren hako
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.
Jihar Nasarawa - Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya bayyana farin cikinsa kan bude masana'antar sarrafa lithium ta kasar Sin mai darajar dala miliyan 200 a jiharsa.
Gwamnan ya bukaci matasan jihar da su shiga kwasa-kwasai na fasaha domin samun damar aiki tare da sabbin kamfanonin hakar ma'adinai na kasar Sin da ke tasowa a yankin.

Kara karanta wannan
Lokacin matasa ya yi: Atiku ya yaba da yadda matashiya 'yar bautar kasa ta soki Tinubu
Gwamna Sule ya yi wannan kira ne a ranar Talata bayan duba ci gaban aikin gina masana'antar Jiuling Lithium Mining Company da ke Endo, karamar hukumar Nasarawa.

Asali: Getty Images
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahoton The Guardian ya bayyana cewa ziyarar gwamnan zuwa wurin ta samo asali ne daga tafiyarsa zuwa kasar Sin, inda ya ziyarci hedikwatar Jiuling da ke Yichun tare da ganawa da shugaban kamfanin, wanda ya yi alkawarin kafa irin wannan masana'anta a jihar Nasarawa.
Ya kamata ku samu horo mai kyau
Sai dai, gwamnan ya bayyana cewa, sai idan al'ummar jihar sun mallaki kwarewar da ake bukata ne za su iya amfana da shigowar kamfanonin hakar ma'adinai na kasar Sin cikin jihar.
Bayan zagayen wurin, Gwamna Sule ya shaida wa manema labarai cewa matasan jihar za su amfana sosai idan suka yi karatun da zai basu damar samun aiki da Jiuling Lithium Mining Company.
A cewarsa:
"Lokacin da na je kasar Sin, na yi kokarin gano yadda wannan masana'anta za ta amfani jihar Nasarawa, al'ummar karamar hukumar Nasarawa, da kuma mutanen yankin Udege. Na tambaye su, suka fara da batun samar da ayyukan yi.
"Sun ce za su dauki ma'aikata daga cikin al'ummarmu, musamman wadanda suka kware a bangaren fasaha, kuma sun yi alkawarin ba su albashi mafi karanci na Naira 500,000. Wannan ne na tabbatar da shi a yanzu.
"Mun hadu da wasu injiniyoyi a wurin. Kiran da nake son yi wa jama'armu shi ne cewa, yawancin ma'aikatan fasaha da muka gani daga wasu jihohi suka fito, wasu daga Nasarawa ne, wasu kuma daga Kogi, Benue da Plateau.
"Duk da cewa ina matukar farin ciki da ganin akwai 'yan asalin jihar Nasarawa a ciki, ina so jama'armu su yi amfani da wannan dama ta yin karatun da zai ba su damar aiki a irin wannan wuri."
Mutanen da suke aiki a kamfanin sun kai 800
Ya kara da cewa fiye da ma'aikata 800 da ke aiki a wurin sun fito daga al'ummomin da ke karbar bakuncin kamfanin.
Ya kara da cewa:
"Idan har akwai isassun kwararrun ma'aikata daga jihar Nasarawa, za su dauke su aiki da farko. Amma idan babu, ba za su dakatar da masana'antarsu ba; za su dauki ma'aikata daga wasu wurare."
Tsarin da kamfanin ya dauko na biyan albashi
A nasa bangaren, Manajan Daraktan Jiuling Lithium Mining Company, Xiong Jin, ya tabbatar da aniyar kamfanin na zuba jarin dala miliyan 200 domin gina daya daga cikin manyan cibiyoyin sarrafa lithium a Endo, jihar Nasarawa.
Ya kuma tabbatar da cewa Jiuling za ta rika biyan sabbin ma'aikata albashin da bai gaza Naira 500,000 ba, yayin da ya fadi cikakkun bayanai kan girman masana'antar.
Sai dai, Jin ya bukaci gwamnatin jihar da ta ba da goyon baya wajen samar da ababen more rayuwa da inganta tsaro a yankin.
Bincike kan hakar ma'adinai a Najeriya
A wani labarin, kasar Faransa ta amince da daukar nauyin bincike kan hakar ma'adinai a Najeriya karkashin Hukumar Kula da Hakar Ma'adinai ta Kasa (NGSA).
An tattauna yadda za a gudanar da hakan ne tsakanin wakilin kasar Faransa da kuma ministan ma'adinai na Najeriya.
Najeriya kasa ce mai tattare da ma'adinai masu yawa, wadanda ke daukar hankalin turawan yamma da ma duniya baki daya.
Asali: Legit.ng