Bayan Dangote, Gwamnati Ta ba AA Rano da Wasu Kamfanoni 5 Izinin Shigo da fetur
- Hukumar NMDPRA ta ba kamfanonin mai guda shida lasisin shigo da tan 720,000 na man fetur daga kasashen waje zuwa Najeriya
- Wannan matakin ya zo ne duk da iƙirarin da hukumar ta yi a baya cewa matatar man Dangote tana samar da kashi 90 na man da ƙasar ke buƙata
- Kamfanonin da aka ba lasisin sun haɗa da NIPCO, AA Rano, Matrix, Shafa, Pinnacle, da Bono, domin tabbatar da tsaron makamashi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Gwamnatin Tarayya, ta hannun hukumar NMDPRA, ta bai wa wasu manyan dillalan mai guda shida lasisin shigo da tan 720,000 na man fetur.
Wannan matakin yana zuwa ne a daidai lokacin da ake samun rahotanni daga hukumar cewa matatar man Dangote yanzu tana samar da kusan dukkan man da Najeriya ke buƙata a kowace rana.

Source: Getty Images
An ba kamfanoni 6 lasisin shigo da fetur
Binciken jaridar Punch ya nuna cewa an rarraba yawan man da kowane kamfani zai shigo da shi kamar haka:
- AA Rano - Tan 150,000.
- Matrix - Tan 150,000.
- NIPCO - Tan 120,000.
- Shafa - Tan 120,000.
- Pinnacle - Tan 120,000.
- Bono - Tan 60,000.
Wannan amincewar ta zo ne bayan a farkon shekarar 2026 hukumar ta bayyana cewa ba ta ba da ko lasisi ɗaya ba na shigo da mai, saboda matatar Dangote tana da ƙarfin biyan buƙatar ƙasar.
Dalilin sake bude kofar shigo da mai
A ranar Alhamis, wani babban jami'in hukumar NMDPRA ya fayyace cewa hukumar ba ta taɓa sa takunkumi kan shigo da mai ba.
Ya jaddada cewa babban burin hukumar shi ne tabbatar da tsaron makamashi domin guje wa ƙarancin mai a nan gaba. Jami'in ya bayyana cewa:
“Ba a taɓa sanya takunkumi kan shigo da mai ba. Matsayar hukumar a bayyane take; tsaron makamashi ga ƙasa. Burinmu shi ne tabbatar da cewa babu wani gibi a tsarin samar da mai. Don haka, haɗa man da ake tacewa a gida da kuma wanda ake shigowa da shi zai ba mu daidaiton da ake buƙata.”

Source: Twitter
Kalubale da kare muradun gida
Idan za a iya tunawa, a watan Maris, tsohon shugaban hukumar NMDPRA, Saidu Mohammed, ya bayyana cewa ƙasar ta daina shigo da fetur, in ji rahoton CED Magazine.
A lokacin da yake karɓar baƙuncin 'yan jarida, Mohammed ya yi gargaɗin cewa akwai wasu masu son maida Najeriya baya zuwa zamanin dogara da man ƙasashen waje.
Duk da waɗannan nasarori na tace mai a cikin gida, wannan sabon mataki na ba da lasisi yana nuna cewa gwamnati tana son samun hanyoyi daban-daban na kiyaye dakile tangarda a tsarin samar da fetur ga ƴan ƙasa.
An sanya harajin shigo da fetur
A wani labari, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta sanya harajin shigo da man fetur da dizil na kashi 15 domin karfafa masana’antun cikin gida.
Ana tunanin sabon tsarin zai iya haifar da karin farashin litar man fetur da N150, duk da cewa gwamnati ta ce tasirin ba zai wuce N100 ba.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya umurci hukumomin da abin ya shafa su fara aiwatar da tsarin nan take, maimakon jiran wa’adin kwanaki 30 da aka tsara.
Asali: Legit.ng

