NNPP Ta Zargi Kwankwaso da Yi Mata Kamun Kazar Kuku, Ta Mika Bukata ga INEC
- NNPP ta zargi Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ci gaba da tsoma baki a harkokin jam’iyyar duk da cewa ya sauya sheka
- Jam’iyyar ta ce wasu ƴaƴan Kwankwasiyya da ya bari a cikinta ne ke ci gaba da shari’o’in da suka shafi jam'iyyar NNPP
- An ji NNPP ta gargadi jam’iyyar NDC da kada ta ba wa Kwankwaso tasiri mai yawa, tana mai cewa hakan na iya jefa ta cikin matsala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – Jam’iyyar NNPP ta zargi tsohon ɗan takararta na shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da ci gaba da shiga harkokin jam’iyyar duk da cewa ya yanke alaka da ita zuwa sabuwar jam'iyya.
Jam’iyyar NNPP ta yi wannan zargi ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaranta na ƙasa, Mista Ogini Olaposi, ya fitar a ranar Talata, 9 ga watan Yuni 2026 a jihar Lagos.

Source: Facebook
A ruwayar jaridar Vanguard, NNPP ta ce Kwankwaso na ci gaba da yin tasiri a cikin jam’iyyar ta hannun wasu magoya bayansa da ake zargin ya bari a cikinta bayan ficewarsa.
NNPP ta daura a kan Rabiu Kwankwaso
Jaridar The Sun ta wallafa NNPP ta yi zargin cewa Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso yana kokarin mamaye jam'iyyar NDC kamar yadda ya yi mata.
Jam’iyyar ta ce:
“Kwankwaso ba wai kawai yana ƙoƙarin karɓe ikon siyasa a NDC ta Kano ba ne, har ila yau yana ci gaba da jan NNPP cikin wasu batutuwa saboda dalilan da shi kaɗai ya sani.”
Ta ƙara da cewa:
"Wasu daga cikin ƴan tafiyar Kwankwasiyya su ne ya bari a cikin NNPP domin su ci gaba da shari’o’in da ya fara.”
Tasirin Kwankwaso ya ragu a Kano – NNPP
NNPP ta kuma yi ikirarin cewa ƙarfin siyasar Kwankwaso a jihar Kano ya ragu matuƙa, tana mai cewa da dama daga cikin manyan magoya bayansa sun koma jam’iyyar APC.
Sanarwar ta ce:
“Ya kamata NDC ta fahimci cewa tsarin siyasar Kwankwaso a Kano a baya yana da ƙarfi sosai, amma a halin yanzu yawancin manyan jagorori a tafiyarsa sun koma APC.”
Jam’iyyar ta kuma zargi Kwankwaso da dattijon ɗan siyasa, Buba Galadima, da cin amanar amincewar waɗanda suka kafa NNPP tare da yunƙurin sake karɓe ikon tafiyar da jam’iyyar.

Source: Facebook
A cewar NNPP:
“Kwankwaso da Galadima sun ci amanar amincewar waɗanda suka kafa jam’iyyar, kuma har yanzu ba su daina yunƙurin yin tasiri domin sake karɓe jagorancinta ba.”
Jam’iyyar ta gargadi NDC da kada ta maimaita abin da ta ce NNPP ta fuskanta, tana mai cewa bai wa Kwankwaso cikakken tasiri a cikin jam’iyyar zai iya zama kashe kai a siyasance.
NNPP ta yi kira ga shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da ya mutunta umarnin kotuna domin tabbatar da shirye-shiryen gudanar da zaɓen shekarar 2027 cikin kwanciyar hankali.
Kwankwaso ya zauna da manyan NDC
A baya, kun samu labarin cewa jagororin ƙungiyar Kwankwasiyya sun gana da shugabannin NDC domin warware saɓanin cikin gida da ya bullo a jihar Kano.
Jagoran NDC, Henry Seriake Dickson, ya gana da masu takun-saƙa a bayan rahoton Rabi'u Musa Kwankwaso zai iya barin jam'iyyar saboda wasu dalilai.
Amma bayan zaman, jamiyyar NDC ta ce ba za ta kakaba 'yan takara ba, kuma har yanzu ba ta fitar da sakamakon zaɓen fitar da gwani a kowace jiha ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


