Yadda Yakin Iran da Isra'ila, Amurka Ya Jawo Matsala ga Tsaron Najeriya
- Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya bayyana manyan abubuwan da suke kawo cikas a yaki da ta'addanci
- Musa ya daura alhakin kan yaƙe-yaƙen Isra'ila da Iran da na Rasha da Ukraine wanda suka matsaloli ga kasar
- Ya buƙaci Najeriya ta fara ƙera kayan tsaro a cikin gida, tare da samar da cikakken bayanan 'yan ƙasa domin taimaka wa hukumomis
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Tsaron Najeriya, Christopher Musa, ya bayyana cewa rikice-rikicen da ke gudana tsakanin Isra'ila da Iran sun jawo matsala ga Najeriya.
Har ila yau, Musa ya ce rigimar Rasha da Ukraine sun sa samun kayan aikin soja ya zama mai matuƙar wahala ga Najeriya da sauran ƙasashe.

Source: Facebook
Ya yi wannan bayani ne yayin da yake gabatar da muhimmin jawabi a taron dabarun al'ummar Najeriya da baje kolin tsaro na shekarar 2026 da aka gudanar a Abuja, cewar Punch.

Kara karanta wannan
Matawalle ya tsage gaskiya, ya ce Allah kadai zai iya magance matsalar tsaron Najeriya
Yadda yakin Iran da Isra'ila ke jawo matsala
A cewarsa, ƙasashen da ke cikin yaƙe-yaƙen suna biyan kuɗaɗe tun kafin a ƙera kayan yaƙin saboda suna da ƙarfin tattalin arziki, lamarin da ke hana sauran ƙasashe samun damar saye.
Ya ce:
"Da yaƙin Ukraine, Rasha, Iran, Amurka da Isra'ila, ya zama da wahala samun kayan aiki. Suna biyan kuɗi tun da wuri saboda suna da kuɗi."
Ministan ya jaddada cewa mafita ita ce Najeriya ta fara ƙera kayan aikin tsaro da take buƙata domin rage dogaro da ƙasashen waje.
Ya yaba wa masana'antun cikin gida da masu ƙirƙire-ƙirƙire a fannin tsaro, yana mai kira ga gwamnati da ta ƙara tallafa musu tare da amfani da kayayyakinsu.

Source: Twitter
Kiran da ministan ya yi ga majalisa
Musa ya kuma yi kira ga Majalisar Dokoki ta ƙasa da ta tallafa wajen samar da cikakken bayanan dukkan 'yan Najeriya a faɗin duniya.
Ya ce samar da irin wannan bayanai zai sauƙaƙa aikin jami'an tsaro, musamman 'yan sanda, wajen gano masu laifi da bibiyar ayyukansu.

Kara karanta wannan
Kungiyar dattawan Arewa ta yi wa Tinubu, Kwankwaso, Atiku, Obi kudin goro kan zaben 2027
A cewarsa:
"'Yan sandan Najeriya na fama saboda babu cikakken bayanan da za su yi amfani da su wajen bin diddigin masu aikata laifuffuka."
Duk da haka, ya yabawa rundunar 'yan sanda kan irin nasarorin da take samu duk da ƙalubalen da take fuskanta, cewar Daily Post.
Ya ce jami'an tsaro ba masu sihiri ba ne, don haka sai al'umma sun ba su bayanai cikin lokaci kafin a samu nasarar dakile laifuffuka.
A cewarsa, talauci, rashin aikin yi da jahilci na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa rashin tsaro a Najeriya.
Ministan ya kuma yi kira da a tsara yadda za a kula da kungiyoyin tsaron al'umma kamar Civilian Joint Task Force domin kauce wa ƙara dagula matsalar tsaro.
Matawalle ya magantu kan matsalar tsaro
An ji cewa Karamin ministan tsaro na kasa, Bello Matawalle, ya ce Allah ne kaɗai zai iya kawo ƙarshen matsalar tsaron da ke addabar Najeriya.
Ya buƙaci 'yan Najeriya su ci gaba da bai wa jami'an tsaro goyon baya tare da addu'o'in samun zaman lafiya mai dorewa.
Matawalle ya zargi wasu 'yan adawa da amfani da matsalar tsaro domin cimma manufofin siyasa yayin da ake tunkarar zaben 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
