Boko Haram: Zulum Ya Saka Dokar Hana Sayar da Man Fetur a Bama
- Gwamna Babagana Zulum ya bada umarnin gaggauta haramta sayar da fetur a fadin karamar hukumar Bama, ciki har da yankin Banki
- Bayanan da gwamnati ta fitar sun nuna cewa matakin na da nasaba da kokarin gwamnatin jihar Borno na dakile ta’addanci a yankin
- Farfesa Babagana Zulum ya yi gargadi da cewa za a hukunta duk wanda aka kama da karya wannan doka ba tare da nuna bambanci ba
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bada umarnin dakatar da sayar da man fetur a fadin karamar hukumar Bama.
Rahotanni sun nuna cewa an saka dokar ne a dukkan sassan karamar hukumar ciki har da garin Bama da Banki, saboda dalilai na tsaro.

Asali: Original
Legit ta tattaro bayanan da gwamnan ya yi ne a cikin wani sako da mai magana da yawunsa, Dauda Iliya ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwa da Dauda Iliya ya fitar a ranar Asabar, gwamnan ya dauki matakin ne biyo bayan tattaunawa da hukumomin tsaro na jihar.
Gwamna Zulum ya bayyana cewa wannan umarni ya fara aiki nan take kuma an dauke shi ne domin kare lafiyar al’umma da karfafa yaki da ta’addanci.
An umarci jami’an tsaro su saka ido
Farfesa Zulum ya bayyana cewa gwamnati ba za ta lamunci karya wannan doka ba, kuma an ba jami’an tsaro umarnin su dauki mataki kai tsaye kan duk wanda ya yi watsi da umarnin.
A cewarsa:
"Ina son na fayyace cewa ba sani ba sabo. Duk gidan mai ko mutum da aka kama ya karya wannan doka za a hukunta shi ba tare da rangwame ba."
Zulum ya jaddada cewa wannan mataki wani yunkuri ne na dakile hanyoyin da ‘yan ta’adda ke bi wajen samun kayayyakin da ke taimaka musu wajen kai hare-hare a jihar.
Gwamnati na neman hadin kan jama’a
Daily Trust ta wallafa cewa gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa na da cikakken kudiri na dawo da zaman lafiya mai dorewa a jihar, kuma hakan na bukatar goyon bayan kowa da kowa.
Ya bukaci al’ummar jihar, musamman mazauna Bama da Banki, da su bada hadin kai ga jami’an tsaro da gwamnatin jihar domin ganin an dakile barazanar tsaro da ke gaban su.
Zulum ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace domin tabbatar da tsaro a jihar Borno.

Asali: Getty Images
Ya jaddada cewa hakan na cikin kokarin ba da kariya ga rayuka da dukiyoyin al’umma da ke zaune a yankunan da hare-hare suka daɗe suna ci gaba da faruwa.
Gwamnonin Arewa za su yi taro kan tsaro
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnonin Arewa za su yi wani taro na musamman a jihar Kaduna domin kokarin shawo kan matsalolin tsaro.
Rahoto ya nuna cewa an kashe mutane akalla 133 a jihohin Arewa da suka hada da Borno, Benue, Yobe da sauransu.
Ana sa ran taron gwamnonin zai mayar da hankali kan samar da hanyoyin warware matsalolin tsaro da wasu matsalolin Arewa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng