Ba a Gama Jimamin Kisan Sojoji ba, Bama Bamai Sun Hallaka Ma'aikata a Borno

Ba a Gama Jimamin Kisan Sojoji ba, Bama Bamai Sun Hallaka Ma'aikata a Borno

  • Ta'addanci kungiyoyin 'yan ta'adda ya rutsa da wasu ma'aikatan hukumar ilimi a 6Borno a daidai lokacin da suka taka bam da aka dasa a kan hanya
  • Blessings Luka da Gideon Bitterleaf, sun mutu bayan wata na’urar fashewa (IED) ta tashi a kan hanyar su daga Damboa zuwa Maiduguri
  • Rahotanni sun bayyana cewa mutanen biyun suna zaune a gaban wata motar Toyota Hiace da ke dauke da mangwaro lokacin da motar ta taka wani bam

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Ma’aikata biyu na hukumar ilimi ta karamar hukumar Damboa sun mutu bayan wani abin fashewa ya tashi da su a ranar Litinin a kan hanyar Damboa zuwa Maiduguri da ke jihar Borno.

An gano mutanen da lamarin ya rutsa da su, sun hada da Blessings Luka da Gideon Bitterleaf, kuma tuni aka tabbatar da rasuwarsu a wajen da bam din ya tashi.

Borno
Bam ya tashi da mota a jihar Borno Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Zagazola Makama, kwararre a kan al'amuran tsaro a yankin tafkin Chadi ne ya tabbatar da afkuwar mummunan al'amarin a sakon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda bam ya kashe ma’aikata a Borno

The Cable ta ruwaito cewa mutanen biyu na zaune ne a gaba cikin wata motar Toyota Hiace dauke da mangwaro lokacin da motar ta taka bam din da ake zargin 'yan ta’adda ne suka dasa a hanya.

Rahotanni sun ce jami’an tsaro sun fara bincike don gano wadanda suka kai harin, kuma an rufe yankin domin gudanar da bincike cikin tsanaki.

Lamarin tsaro na kara kamari a Borno tun bayan da gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum ya sanar da gwamnatin tarayya da 'yan Najeriya cewa Boko Haram ta dawo da karfinta.

Ana samun karuwar kashe-kashe a Borno

A ‘yan kwanakin nan, ana samun karuwar fashewar na’urorin IED a jihar Borno, yayin da ‘yan ta’adda ke kaddamar da sababbin hare-hare babu kakkautawa.

A ranar 9 ga Mayu, yara biyar sun jikkata bayan wani bam ya tashi a karamar hukumar Mafa da ke jihar, lamarin da ya tayar da hankulan mazauna yankin.

Borno
Mutum 2 ne suka mutu bayan motarsu ta taka bam Hoto: @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Akalla mutane 26 sun mutu, wasu uku kuma sun jikkata bayan fashewar wani bam a ranar 29 ga Afrilu a kan hanyar Rann–Kala Balge–Gamboru Ngala.

Sannan a ranar 12 ga Afrilu, matafiya takwas sun mutu bayan wani bam ya tashi a kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa.

A ranar 21 ga Maris kuma, fasinjoji hudu sun mutu, wasu hudu kuma sun jikkata bayan wani bam ya tashi karkashin wata motar haya a karamar hukumar Biu da ke jihar.

Boko Haram ta kai hari a Borno

A wani labarin, mun ruwaito cewa ana zargin ‘yan ta’addan Boko Haram da kai wani mummunan hari kan sansanin sojojin Najeriya da ke karamar hukumar Marte a jihar Borno.

Majiyoyi daga cikin mutanen yankin da kuma na tsaro sun tabbatar da cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 3.00 na daren Litinin, inda aka yi artabu tsakanin ‘yan ta’addan da sojoji.

An bayyana cewa ‘yan ta’addan sun yi galaba a harin, suka kashe sojoji da dama, sannan sun kama wasu da ransu, tare da nausawa maboyarsu, har yanzu ba a fadi adadinsu ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.