Akpabio: Farfesan da Kotu Ta Daure kan Murde Zabe Ya Ki Zaman Kurkuku

Akpabio: Farfesan da Kotu Ta Daure kan Murde Zabe Ya Ki Zaman Kurkuku

  • An gano cewa Farfesa Peter Ogan da kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin da aka yi masa kan murde zabe na yawo a gari abinsa
  • Wannan na zuwa ne bayan kotuna biyu sun tabbatar masa da daurin shekaru uku saboda laifin bayyana sakamakon zaben bogi a Akwa Ibom
  • Sakamakon da ya sanar na bogi a kananan hukumomin Anam da Etim Ekpo a jihar Akwa Ibom ya tabbatarwa Godswill Akpabio nasara a zaben 2019

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Akwa Ibom – Peter Ogban, wani Farfesa da aka tabbatar da laifinsa tare da yanke masa hukuncin dauri na shekara uku saboda murde zaben ba ya kurkuku.

An tabbatar da cewa Farfesa Oghan ya murde zabe saboda ya tabbatarwa da shugaban majalisar dattawa na yanzu, Godswill Akpabio, nasara a 2019.

Akpabio
Farfesan da ya murdewa Akpabio zabe bai yi zaman kurkuku ba Hoto: Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

Premium Times ta wallafa cewa bayan da kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin da aka yanke masa, yawancin 'yan Najeriya na zaton Farfesa Ogban yana zaune a gidan yari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar 30 ga Afrilu, kotun daukaka kara da ke Kalaba ta tabbatar da hukuncin da kotun farko ta yanke masa na daurin shekara uku a gidan yari kan laifin.

An kama Farfesa da laifin murde zabe

Sahara Reporters, ta ruwaito babbar kotun jiha a garin Uyo a ranar 25 ga Maris, 2021, ta samu Farfesa Oghan da laifin fadin sakamakon zaben bogi a karamar hukumar Oruk Anam da Etim Ekpo a Akwa Ibom.

Bayan yanke hukuncin, an dauke Ogban daga kotun Uyo zuwa gidan yari na tarayya da ke Ikot Ekpene domin fara zaman daurin.

Akwa Ibom
An kama Farfesa Oghan da murde zaben kananan hukumomin AKwa Ibom 2 Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Sai dai binciken ya nuna cewa farfesan bai shafe fiye da watanni hudu a gidan yari ba saboda a ranar 12 ga Yuli, 2021, wani alkalin kotun jiha da ke Ikot Ekpene, Pius Idiong, ya ba da belinsa.

Farfesan da ya murde zabe ya daukaka kara

A wancan lokaci, Farfesa Ogban ya daukaka kara ne kan hukuncin da aka yanke masa, daga baya kuma, kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin daurin shekara uku da aka yi masa.

Rahoton ya kara da cewa wani lauya da ya halarci zaman kotun daukaka kara ya bayyana cewa Farfesa Ogban bai halarci zaman kotun ba a lokacin da aka yanke hukunci.

Ya ce:

“Ma’aikatan gidan yari na Najeriya ya kamata su tabbatar sun gabatar da Farfesa Ogban a kotu a lokacin yanke hukuncin. Kuma daga nan ne ya kamata su mayar da shi kai tsaye zuwa gidan yarin Ikot Ekpene,” in ji lauyan.

Da aka tuntubi mai magana da yawun Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya a Akwa Ibom, Richard Metong, ya ce bai da tabbacin ko Ogban yana daya daga cikin wadanda ke tsare a gidajen yarin jihar.

Ya bukaci lokaci don bincike, amma bai sake tuntubar wakilin jaridar ba, kuma bai amsa kira ba daga baya.

Akpabio ya caccaki Obi

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya mayar da martani mai zafi kan tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi kan sukar Tinubu.

Martanin Akpabio ya biyo bayan kalaman da Obi ya yi a taron binne Edwin Clark, inda ya yaba da rayuwar marigayin, amma ya kara da cewa abin takaicin shi ne ikin ‘yan mazan jiya ya tafi a iska.

Shugaban majalisar ya ce mulkin ƙasa ba aikin kwaikwayo ba ne, kuma ya kamata Obi ya nuna kwarewa da shugabanci tun daga gida kafin neman jagorancin ƙasa baki ɗaya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.