INEC na Shirin Sauya Tsarin Zabe, ana Son Marasa Katin PVC Su Kada Kuri'a a 2027

INEC na Shirin Sauya Tsarin Zabe, ana Son Marasa Katin PVC Su Kada Kuri'a a 2027

  • Hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta bayyana shirin halatta kada ƙuri’a ba tare da katin zabe na dindindin watau PVC ba a zaɓen 2027
  • Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce ana nazarin amfani da fasaha wajen sauƙaƙa tantance masu zaɓe ta amfani da takardu da kwamfuta
  • INEC ta bayyana cewa matakin zai rage kashe kuɗi, sauƙaƙa jigilar kayayyaki da kuma kawar da matsalar mallakar PVC don hana mutane kada ƙuri’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) na duba yiwuwar bai wa ‘yan Najeriya damar kada ƙuri’a ba tare da amfani da katin PVC ba a zaɓen 2027.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya fara maganar tun a watan Disamban 2024 yayin wani taron tattaunawa da kwamishinonin zaɓe na jihohi da aka gudanar a Abuja.

Shugaban INEC
INEC son ba marasa kati damar kada kuri'a a 2027. Hoto: INEC Nigeria
Asali: Twitter

Punch ta wallafa cewa hukumar ta ce dole ne a samu sauyi a dokokin zaɓe na ƙasa kafin a aiwatar da tsarin fasahohi wajen tantance masu kada ƙuri’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

INEC na son daina amfani da PVC

Farfesa Yakubu ya ce duk da cewa PVC za ta ci gaba da amfani ga waɗanda ke da katin, akwai yiwuwar masu zaɓe su iya amfani da takardun da INEC za ta fitar don kada kuri'a.

Shugaban INEC ya ce:

“Wadanda ke da PVC za su ci gaba da amfani da shi, amma ana duba yiwuwar amfani da takardun INEC domin tantance masu zaɓe,”

Ya ƙara da cewa amfani da tsarin tantance masu zaɓe da BVAS ya ba da dama wajen rage dogaro da PVC kaɗai a matsayin hanyar tantance masu zaɓe.

Fa'idar daina amfani da kati wajen zabe

Farfesa Yakubu ya ce tsarin zai taimaka wajen rage kashe kuɗi da kuma kawar da matsalolin da ke tattare da raba katin PVC, da kuma soke hana kada kuri'a ga wanda ba shi da PVC.

Shugaban INEC ya bayyana cewa:

“Wannan zai taimaka wajen rage kuɗin da ake kashewa da kuma magance matsalolin tattarawa da raba PVC.
"Haka kuma, za a hana mummunar dabi’ar sayen katin mutane domin hana su kada ƙuri’a,”

Bukatar gyara dokar zabe ta kasa

A wata hira da manema labarai a ranar Laraba, mai magana da yawun shugaban INEC, Rotimi Oyekanmi, ya ce sai an yi gyara a dokar zaɓe kafin a aiwatar da canjin.

The Cable ta wallafa cewa Rotimi Oyekanmi ya ce:

“Ba matsayar hukumar kaɗai ne ke da muhimmanci ba, dole ne a duba abin da dokar da ake amfani da ita a yanzu ta tanada. Don haka, sai an yi gyara a dokar kafin a canza tsarin,”
Zaben Najeriya
Hukumar INEC na shirin kawo sauyi a dokar zabe. Hoto: Getty Image
Asali: Twitter

2027: Tinubu ya bukaci a jira sanarwar INEC

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya bukaci a jira hukumar INEC ta sanar da fara yakin neman zabe kafin fara masa kamfen.

Bola Tinubu ya yi magana ne bayan an fara saka allunan yakin neman zaben shi a wasu jihohin Najeriya tun gabanin kada gangunan siyasa.

Shugaban kasar ya ce ya barranta da duk wani kokarin fara masa kamfen da ya saba dokar kasa da wasu mutane ke yi ma shi a yanzu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng