Rikicin APC: Gwamna Namadi Ya Dakatar da Hadiminsa, Ya Mayar da Wani Bakin Aiki
- Gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi, ya dakatar da wani mataimakinsa na musamman a karamar hukumar Auyo a jihar
- A lokaci guda, gwamnan ya mayar da wani mataimaki da aka dakatar a baya zuwa bakin aikinsa a yankin Kafin Hausa
- Matakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da samun rikice-rikicen siyasa a cikin jam’iyyar APC bayan zaben fitar da gwani a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Jigawa – Gwamnan jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da dakatar da wani mataimakinsa musamman kan sa ido a harkokin ilimi a karamar hukumar Auyo
Haka kuma, Gwamnatin Jigawa ga sanar da mayar da wani mataimaki da aka dakatar a baya bakin aikinsa a karamar hukumar Kafin Hausa.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta ruwaito cewa wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Bala Ibrahim, ya fitar.
Haka kuma jami’in hulda da jama’a na ofishinsa, Isma’ila Dutse, ya rabawa manema labarai a Dutse ranar Alhamis, 4 ga watan Yuni, 2026.
Ana samun sabanin siyasa a APC
Rahotanni sun nuna cewa sabon matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun rashin jituwar siyasa a cikin jam’iyyar APC mai mulki a Jigawa bayan kammala zabukan fitar da gwani na jam’iyyar.
A cewar sanarwar, gwamnan ya amince da dakatar da Sule A. Musa, wanda ke matsayin Mataimaki na musamman kan a sa ido a harkokin ilimi na karamar hukumar Auyo.
Kafin dakatarwar, Sule A Musa na da alhakin bibiyar ayyukan ilimi da kuma tabbatar da halartar malamai a makarantu da ke fadin karamar hukumar
Sai dai gwamnatin jihar ba ta bayyana takamaiman dalilin da ya jawo dakatar da shi ba a cikin sanarwar da ta fitar.
Gwamnatin Jigawa ta dawo da hadimin gwamna
A wani bangare kuma, Gwamna Umar Namadi ya janye dakatarwar da aka yi wa Basiru Abdullahi, wanda aka fi sani da “Optimistic”.
Gwamnati ta ce an mayar da shi kan mukaminsa na Mataimaki na musamman kan sa ido a harkokin lafiya na karamar hukumar Kafin Hausa.

Source: Facebook
Ana sa ran Abdullahi zai koma bakin aikinsa nan take bayan janye dakatarwar. Sakataren gwamnatin jihar ya jaddada cewa duka dakatarwar da kuma mayar da mukamin sun fara aiki nan take.
Masu bibiyar harkokin siyasa sun alakanta yawaitar dakatarwa da mayar da wasu jami’an siyasa bakin aiki da tasirin rikicin da ya biyo bayan zabukan fidda gwani na APC,.
Sai dai ita gwamnatin jihar Jigawa ba ta danganta sababbin matakan da wannan rikicin a hukumance ba.
Gwamnan Jigawa ya dakatar da hadimansa
A baya, kun samu labarin cewa wasu daga cikin hadiman gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, sun fuskanci dakatarwa ba tare da bata lokaci ba saboda wasu dalilai .
Gwamna Umar Namadi ya ba da umarnin dakatar da hudu daga cikin hadimansa har sai baba ta gani bisa wasu zarge-zarge a cikin wani umarni da aka bayar a makon nan.
Lamarin ya shafi Abbas Makama, babban mataimaki na musamman kan kula da ambaliyar ruwa I, Salisu Muhammad, wanda aka fi sani da Rosy Auyo, mataimaki na musamman kan Harkokin kasuwan
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


