Gwamnati Ta Kashe N3bn don Biyawa Daliban Kano Kudin NECO da Wasu Jarrabawa
- Gwamnatin Kano ta kashe sama da Naira biliyan uku domin daukar nauyin jarrabawar NECO da NABTEB
- Za ta aiwatar da haka ne bayan 75% na daliban da suka rubuta jarrabawar tantancewa da ake kira 'qualifying' sun yi nasara
- Gwamnati ta ce wannan na daga cikin matakan dokar ta bacin ilimi da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ayyana a baya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnatin Kano ta kashe sama da N3bn domin daukar nauyin dalibai 141,175 da suka ci jarrabawar tantancewa ta 2024.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince da kashe kudin ne domin daliban su samu damar rubuta jarrabawar kammala sakandare ta NECO, NABTEB da NBAIS ta bana.

Asali: Facebook
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Ibrahim Adam, ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce Kwamishinan Ilimi na jihar, Ali Haruna Makoda, ya bayyana cewa ma’aikatar ilimi ta fitar da sakamakon jarrabawar tantancewar da daliban sakandare suka rubuta.
Daliban Kano sun ci jarrabawar tantancewa
Jaridar Punch ta ruwaito cewa 75% na daliban da suka ci jarrabawar suna karatu ne karkashin Hukumar Kula da Malamai da Hukumar Makarantun Kimiyya da Fasaha a jihar.
Sanarwar ta kara da cewa dukkaninsu kuma sun cancanci su zauna jarrabawar kammala sakandare na NECO, NABTEB da NBAIS (ga daliban Larabci).

Asali: Facebook
Kwamishinan ya bayyana cewa daliban da gwamnatin Kano za ta biya wa kudin jarrabawa su ne wadanda suka samu akalla darussa biyar da suka yi nasara da sakamako mai kyau.
Ya ce:
“Wadannan dalibai suna karatu ne a karkashin Hukumar Kula da Malamai da Hukumar Makarantun Kimiyya da Fasaha, inda 75% daga cikinsu suka cancanci su zauna jarrabawar kammala sakandare ta NABTEB, NECO da NBAIS (ga masu karatun Larabci).
“Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf za ta biya kudin jarrabawa ga wadanda suka samu a kalla darussa biyar da suka ci da sakamako mai kyau."
Iyayen Kano za su samu rangwame
Kwamishinan ya bukaci shugabannin makarantun sakandare da daraktoci su sanar da dalibansu sakamakonsu, domin gwamnati ta ci gaba da aiwatar da biyan kudin jarrabawar.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa tun daga lokacin da Gwamna Abba ya hau mulki, gwamnatinsa ta biya kudin jarrabawar WAEC, NECO, NABTEB da NBAIS ga daliban da ba su da karfi a Kano.
Haka kuma, gwamnatin ta biya bashin da aka gada na kudin jarrabawar WAEC, NECO da NABTEB da suka taru kafin hawanta mulki.
A cewar sanarwar, wannan wani bangare ne na kudurin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ayyana dokar ta baci a fannin ilimi, da kuma kokarin rage yawan yara marasa zuwa makaranta.
Gwamnatin jihar Kano na inganta ilimi
A baya, mun ruwaito cewa gwamnatin Kano ta dauki matakai domin farfado da harkar ilimi a jihar, daga ciki har da daukar sababbin malamai da kuma gina dakunan bincike a makarantu.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce wannan mataki yana daya daga cikin kudurinsa na ganin ilimi ya inganta a Kano, tare da tabbatar da cewa jihar ta yi fice a tsakanin takwarorinta.
Ya ce gwamnatinsa ta gano cewa akwai gagarumar matsala a bangaren ilimi, da suka hada da karancin malamai, rashin horarwa na yau da kullum, da kuma rashin kayo da koyarwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng