An Fara Rabawa Talakawa ATM domin Samun Tallafin N75,000 a Zamafara

An Fara Rabawa Talakawa ATM domin Samun Tallafin N75,000 a Zamafara

  • Gwamna Dauda Lawal ya ƙaddamar da rabon katin cire kuɗi ga sama da mutum 400,000 a karkashin tsarin tallafin kuɗi na Bankin Duniya
  • An gudanar da bikin kaddamar da shirin ne a karamar hukumar Tsafe a ranar Litinin, inda aka tabbatar da raba N75,000 ga duk wanda ya cancanta
  • Gwamnan ya bukaci wadanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da kuɗin wajen zuba jari da dogaro da kai, maimakon kashe su ta wasu hanyoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Zamfara - A ci gaba da kokarinsa na taimakawa marasa galihu da rage talauci a Zamfara, Gwamna Dauda Lawal ya ƙaddamar da rabon katin ATM ga dubban ‘yan asalin jihar.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an kaddamar da shirin ne a karkashin tsarin tallafin kuɗi na bankin duniya.

Zamfara
Gwamnatin Zamfara ta fara raba tallafin kudi. Hoto: Sulaiman Bala Idris
Asali: Facebook

Mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya wallafa yadda aka kaddamar da shirin a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gudanar da bikin kaddamar da shirin ne a karamar hukumar Tsafe, inda aka ce sama da mutum 400,000 ne za su amfana da wannan shiri da Bankin Duniya ke daukar nauyi.

Sulaiman Bala Idris ya ce kowanne daga cikin waɗanda suka cancanta zai samu N75,000 a matsayin tallafin dogaro da kai da inganta rayuwa.

Mutum 279,000 sun cika sharudan samun tallafi

Yayin da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Lawal ya bayyana cewa fiye da mutane 279,534 sun cika ka’idar da ake bukata don karɓar tallafin da ya kai N75,000.

Ya ce sauran mutane za su samu damar amfana da shirin nan gaba kadan idan an kammala tantance su.

Gwamnan ya ce:

“Wannan shiri wata dama ce da gwamnati ta samar domin mutane su samu damar gina kansu da iyalansu kuma su taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin ƙasa da na jiha,”

Gwamna Lawal ya bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin da su kauce wa kashe kudin a abubuwan da ba su da amfani, su mayar da hankali kan sana’o’i da ayyukan dogaro da kai.

Tallafin Zamfara zai karfafa tattalin jihar

Gwamnan ya bayyana cewa wannan shiri wani mataki ne na tabbatar da cewa marasa galihu sun samu damar farfadowa daga matsin tattalin arziki da ake ciki.

Ya ce gwamnatin sa ba za ta daina haɗin gwiwa da hukumomi da ƙungiyoyi masu zaman kansu ba domin ciyar da jihar gaba.

Dauda
Gwamnan Zamfara ya bukaci yin aiki da kudin tallafin da ya raba yadda ya dace. Hoto: Sulaiman Bala Idris
Asali: Facebook

A karshe, gwamna Lawal ya gode wa gwamnatin tarayya da ofishin gudanar da tallafin kuɗi na ƙasa da sauran abokan haɗin gwiwa bisa jajircewar su wajen ganin an cimma nasarar shirin.

Matawalle ya ba da tallafin N5m a Zamfara

A wani rahoton, kun ji cewa ministan tsaro, Bello Matawalle ya mika tallafin Naira miliyan 5 ga iyalan marigayi Alkali Salihu Sulaiman.

Baya ga kudin, an ruwaito cewa ministan ya mika tallafin kayan abinci da sauran abubuwan rayuwar yau da kullum.

Hakan na zuwa ne bayan da 'yan bindiga masu garkuwa da mutane suka kashe Alkali Salihu Sulaiman da wasu 'ya'yansa a daji.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng