Rikici Ya Barke a APC a Legas, an Nemi Agajin Matar Tinubu

Rikici Ya Barke a APC a Legas, an Nemi Agajin Matar Tinubu

  • Rikici ya barke a jam’iyyar APC reshen Jihar Legas kan zargin kakaba ‘yan takara a zabukan kananan hukumomi da ke tafe
  • ‘Yan jam’iyya da dama sun zargi jiga-jigan jam’iyyar da yunkurin hana sahihin zabe ta hanyar ɗora 'yan takarar da suka so
  • Zanga-zanga da koke-koke sun barke a wasu kananan hukumomi kamar Ojokoro da Yaba saboda zargin murde tsarin yarjejeniya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Legas - Ana cikin shirin gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Legas, amma rikici ya kunno kai a jam’iyyar APC.

An fara samun sabani ne yayin da mambobi da dama suka fara kokawa kan abin da suka kira yunkurin tilasta 'yan takara ba tare da bin tsarin zabe ba.

Ganduje
Rikici ya barke a APC a Legas kan zaben 'yan takara. Hoto: Salihu Tanko Yakasai
Asali: Twitter

Punch ta wallafa cewa a ranar 12 ga watan Yuli ne hukumar zabe ta jihar Legas (LASIEC) ta tsara gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi guda 57 da kuma kansiloli 376 a fadin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa jam’iyyar APC ta amince da tsarin yarjejeniya wajen fitar da 'yan takara a matakin farko na zaben fidda gwani da aka shirya.

Sai dai duk da yarjejeniyar, abubuwa da dama sun janyo sabani da fargaba a tsakanin 'yan takara da mambobin jam’iyyar.

Lagos: An yi rikici a APC a Ojokoro

Kungiyar dattawan APC a yankin Ojokoro ta tantance 'yan takara uku inda Mobolaji Sanusi ya fito a matsayin dan takarar da aka cimma matsaya a kansa.

Sakamakon hakan ya samu sahalewar manyan jam’iyyar kamar tsofaffin 'yan majalisar wakilai, Ipoola Omisore da Adisa Owolabi, da kuma shugaban karamar hukumar mai ci, Idowu Tijani.

Amma cikin kwanaki bayan sanarwar, wata sabuwar matsala ta tashi bayan gungun 'yan jam’iyyar suka fitar da wani dan takara daban, Rosiji Yemisi, wanda hakan ya dagula lamarin.

Remi Tinubu
An nemi Remi Tinubu ta sasanta rikicin APC a Legas. Hoto: Aso Villa
Asali: UGC

Wani mamba daga cikin masu adawa da wannan sabon mataki ya bayyana cewa ana kokarin tilasta dan takarar da ba dan yankin ba ne.

The Cable ta rahoto cewa mamban ya ce wanda ake zargin yana da goyon bayan Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Legas, Mudashiru Obasa.

Rikicin APC: An yi zanga-zanga a Yaba

A Yaba LCDA ma wasu daga cikin ‘yan siyasa da al’ummar yankin sun fito fili sun koka kan kokarin sauya sunan wanda ya yi nasara a tantancewa da wanda ya zo na 11.

An bayyana cewa William Babatunde ya samu maki 85 cikin 100, yayin da Babatunde Ojo ya samu 65, amma ana kokarin sauya sunansa da na Ojo a matsayin dan takara.

Wata kungiya da ta kunshi masu kada kuri’a da jiga-jigan siyasa a yankin karkashin jagorancin Amoo Ismail sun aika takarda ga matar Shugaban Kasa, Remi Tinubu, da bukatar ta shiga tsakani.

Sheikh Dalha ya fita daga jam'iyyar APC

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban malamai a Izala, Sheikh Dalhatu Abubakar Hakimi ya fita daga APC.

Sheikh Dalha ya bayyana haka ne a cikin wata takarda da ya tura wa shugaban APC na mazabar shi da ke Tafawa Balewa a Bauchi.

Malamin ya yi wa jam'iyyar APC takarar dan majalisar tarayya a shekarar 2019 amma bai samu kai wa ga nasara ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng