Abu Ya Lalace: An Zargi Sarakuna da Karɓar Shanu, Kuɗi domin Taimakawa Ƴan Bindiga

Abu Ya Lalace: An Zargi Sarakuna da Karɓar Shanu, Kuɗi domin Taimakawa Ƴan Bindiga

  • Mazauna jihar Delta sun zargi wasu sarakuna da ‘yan sa-kai da hada kai da makiyaya masu garkuwa da mutane saboda son kudi
  • Gwamna Oborevwori yana shirin daukar mataki kan garkuwa, yayin da majalisa ke sake duba dokar rundunar tsaron al’umma
  • Wasu sarakuna sun musanta zargin, yayin da wasu shugabanni suka ki karbar kyautar N10m da saniya daga Fulani don samun fili

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Asaba, Delta - Jama'a da suka hada da masu fafutuka sun zargi wasu sarakunan gargajiya da 'yan sa-kai da hada kai da yan bindiga masu garkuwa saboda kudi.

Mazauna da suka yi kokarin dakile garkuwa sun gano cewa wasu Fulani suna ba sarakuna kudi da shanu don samun mafaka a dazuka.

Ana zargin sarakuna da taimakawa yan bindiga
An zargi sarakuna da karɓar shanu da kudi daga yan bindiga a Delta. Hoto: Legit.
Asali: Original

'Yan bindiga: Ana zargin sarakuna a Jihar Delta

Vanguard ta ce Gwamna Oborevwori ya dauki matakai na shawo kan matsalar, kuma yana shirin kaddamar da tsari mai ƙarfi don dakile garkuwa da mutane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gano cewa wasu Fulani dauke da bindiga suna shiga dazuka su hada kai da na gari su boye, daga nan su sace mutane don kudin fansa.

Wani ya ce ‘yan sa-kai da matasa suna bayar da bayanai ga ‘yan garkuwa, su kuma su karbi rabonsu daga kudin fansa.

Ya ce:

“Wasu daga cikinmu da sarakunanmu da suka ba su fili suna taimaka wa masu garkuwa."
Ana zargin sarakuna da alaka da yan bindiga
An zargi sarakuna da goyon bayan yan bindiga a Delta. Hoto: Hon. Sheriff Oborevwori.
Asali: Twitter

Wani basarake ya wanke 'yan uwansa

Wani dan rajin kare hakkin dan Adam ya ce idan Fulani suka zauna dazuka na tsawon watanni, sun riga sun biya sarakuna kudi.

“Muna biya sarakunanku, amma wasu mazauna ba su sani ba. Su tambayi sarakunan, domin mun biya.
"Sarakuna su kan ce Fulani su taimaka musu kiwon shanun da aka ba su da cin hanci, shiyasa ba sa son su bar dazuka."

- Cewar wani mazaunin yankin

Tsohon kwamishinan ‘yan sanda, Hafiz Inuwa ya tabbatar da cewa sarakuna na karbar kudi da shanu daga Fulani su barsu su kafa sansani.

Inuwa ya ce:

“Idan mu na son gaskiya, sai mu tambayi wadanda suke bai wa Fulani fili domin su kafa sansaninsu.”

Wani basarake, Pere Luke, ya ce kwamishinan ‘yan sanda ya sanar da su cewa sarakuna da dama sun bai wa Fulani filaye da ake gardama a kai.

“Kwamishinan ya kuma ce Fulani sun mamaye kungiyoyin sa-kai na gari, suna bayar da bayanai ga ‘yan garkuwa."

Wani basarake da aka ambata ya karyata zargin da aka yi masa, ya ce:

“Ban taba ba su fili ba, su kawo hujja idan suna da ita.”

Ya zargi wasu 'yan sanda da taimaka wa Fulani, yana cewa wasu daga cikinsu suna karbar fili, su binciki asusun ajiyarsu da kadarorinsu.

Rashin tsaro: Hadimin gwamna ya yi murabus

Kun ji cewa hadimin Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta, Harrison Gwamnishu, ya yi murabus daga muƙaminsa saboda matsalar tsaro.

Harrison Gwamnishu ya ce ya miƙa ƙorafe-ƙorafe tare da shawarwarin yadda za a magance rashin tsaro amma gwamna ya yi watsi da su

Ya ce a matsayinsa na ɗan gwagwarmaya mai kokarin kare haƙkin al'umma, ya yi murabus ne domin jawo hankalin gwamnan Delta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.