'Yan Ta'addan Boko Haram Sun ga Ta Kansu, Babban Hafsan Sojojin Kasa Ya Koma Borno

'Yan Ta'addan Boko Haram Sun ga Ta Kansu, Babban Hafsan Sojojin Kasa Ya Koma Borno

  • Dakarun sojojin Najeriya na ci gaba da ƙara ƙaimi domin ganin sun murƙushe ƴan ta'addan Boko Haram da ISWAP a yankin Arewa maso Gabas
  • Babban hafsan sojojin ƙasa (COAS), Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya koma jihar Borno tare da manyan kwamandojinsa
  • Komawarsa Borno na da nasaba da ƙoƙarin da sojoji suke yi na ganin sun murƙushe ƴan ta'adda da suka daɗe suna addabar jama'a

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Babban hafsan sojojin ƙasa (COAS), Laftanar Janar Olufemi Oluyode, ya koma birnin Maiduguri, na jihar Borno.

Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya koma jihar Borno ne tare da manyan kwamandojinsa a wani ɓangare na ƙoƙarin sake tsara dabarun yaƙi da ta’addanci a yankin Arewa maso Gabas.

Babban hafsan sojojin kasa ya koma Borno
Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya koma jihar Borno Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Zagazola Makama ya ruwaito cewa komawar hafsan sojojin ta zo ne a daidai lokacin da ake ƙara ƙaimi wajen ƙaddamar da hare-hare kan ragowar ƴan ta'addan Boko Haram da ISWAP da ke barna a yankin Tafkin Chadi da dajin Sambisa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban hafsan sojojin ƙasa ya koma Borno

Laftanar Janar Oluyode, wanda ya kwashe kwanaki uku a fagen daga, na jagorantar wata tawaga mai ƙarfi ta manyan hafsoshin soja domin gudanar da tantancewa da kuma nazari kan ayyukan da ke gudana ƙarƙashin shirin Operation Hadin Kai.

Wata majiya daga rundunar sojoji ta bayyana cewa babban hafsan sojojin yana amfani da wannan ziyara domin ganawa da kwamandoji, dakarun da ke fagen daga da sauran manyan hafsoshin soja domin ƙarfafa haɗin gwiwa a yaƙin da ake da ta’addanci.

“COAS yana nan a fagen daga. Kasancewarsa a wurin yaƙi na nuna gaggawar da ke akwai wajen sake fasalta ayyukan sojoji da kuma tabbatar da cewa an tallafawa dakarunmu ta kowace hanya."

- Wata majiya

Janar Oluyode ya kuma gudanar da zaman sirri da kwamandojin filin daga, sashen leken asiri da sauran ɓangarori rundunar JTF domin inganta dabaru na rushe ragowar sansanonin ƴan ta’adda.

Ana sa ran wannan ziyara za ta ƙara ƙarfafa gwiwar dakarun sojoji da kuma tabbatarwa da al’ummar yankin cewa rundunar sojojin Najeriya za ta ci gaba da ƙoƙari wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Olufemi Oluyede
Babban hafsan sojojin kasa ya koma fagen daga a Borno Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Rundunar sojoji ta tabbatar da komawar COAS Borno

Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da cewa babban hafsan sojojin yana fagen daga a jihar Borno a wani saƙo da ta sanya a shafinta na X.

Ta bayyana cewa Laftanar Janar Olufemi Oluyede yana jagorantar dakarun sojoji da ke a fagen daga.

Ƴan Boko Haram sun hallaka sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan ta'addan Boko Haram sun hallaka jami'an tsaro na sojoji a jihar Borno.

Ƴan ta'addan sun hallaka wani Kyaftin tare da soja guda ɗaya a wani hari da suka kai a ƙauyen Izge da ke ƙaramar hukumar Gwoza.

A yayin artabun da aka yi, dakarun sojoji sun samu nasarar hallaka wasu daga cikin ƴan ta'addan tare da ƙwato makamai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng