Guguwa Mai Karfin Gaske Ta Hallaka Mutane, Ta Lalata Gidaje fiye da 1,200 a Borno
- Akalla mutane hudu ne aka tabbatar sun rasu, yayin da gidaje sama da 1,200 suka lalace sakamakon guguwa mai karfi a Borno
- Gwamna Babagana Zulum ya bai wa iyalan kowane mamaci tallafin N500,000 tare da yin alkawarin gyara gidajen da abin ya shafa
- Gwamnan ya gargaɗi mazauna jihar kan dabi'ar sare bishiyoyi, yana mai cewa hakan na janyo guguwa da matsalolin muhalli
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Borno - Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya kai ziyarar jaje garin Bama domin ganawa da waɗanda mummunar guguwa ta rutsa da su, wadda ta shafi gidaje da dama.
Shugaban ƙaramar hukumar Bama, Babagana Barma, wanda ya karɓi gwamnan, ya bayyana cewa aƙalla mutane huɗu ne suka rasa rayukansu a wannan mummunar guguwa.

Source: Getty Images
Guguwa ta kashe mutane a jihar Borno
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Babagana Barma ya kuma shaida wa Zulum cewa gidaje sama da 1,200 suka lalace sakamakon wannan iftila'i.
Da yake jajantawa Bama bisa wannan iftila'i, Gwamna Zulum ya bayyana cewa:
“Ya zama dole mu daina sare bishiyoyi ba gaira ba dalili. Wannan shi ne babban dalilin da ke ƙara ƙarfin guguwa da matsalolin muhalli da muke fuskanta. Akwai dokoki a ƙasa, kuma akwai buƙatar mu tabbatar an aiwatar da su yadda ya kamata.”
Yayin ziyarar tasa, Gwamna Zulum ya sanar da bayar da tallafin gaggawa, wanda ya haɗa da kuɗi Naira 500,000 ga iyalan kowane mamaci da guguwar ta yi ajali.
Haka kuma, ya ba da umarnin gudanar da bincike na gaggawa domin tantance girman barnar da aka yi a yankunan da abin ya shafa.
Za a fara gyara gidaje a Borno
Mai girma Gwamna Zulum ya tabbatar wa mazauna Bama cewa za a bai wa kowane gida tallafi gwargwadon yadda barnar ta shafe shi.
Bugu da ƙari, gwamnan ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na mayar da dukkan yan gudun hijira zuwa garuruwansu na asali cikin mutunci da tsaro.
Ya buƙaci hukumomin da abin ya shafa da su hanzarta tantancewa domin fara aikin gyara gidajen da iskar ta kwashe wa rufi.
Mazauna garin sun shaida wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 3:00 na yammacin ranar Juma'a, in ji rahoton The Guardian.

Source: Twitter
Halin da Bama ta shiga sakamakon guguwa
Wani mazaunin yankin, Mala Bashir, ya bayyana cewa yankunan Gwange da sansanin yan gudun hijira ne suka fi fuskantar barna, inda ya yi iƙirarin cewa adadin waɗanda suka rasu ya kai mutane 10, yayin da da dama suka ji rauni.
Wani kuma mai suna Modu Sheriff ya bayyana cewa suna tsaka da shirin sallar Azahar ne kwatsam iska mai ƙarfi ta mamaye garin, ta riƙa tumbuke bishiyoyi tare da kwashe rufin gidajen mutane.
Wannan ibtila'i ya bar mazauna garin cikin mawuyacin hali, yayin da suke fatan samun tallafi daga gwamnati da sauran ƙungiyoyin agaji.
Jihohi 11 za su fuskanci iska mai karfi
A wani labari, mun ruwaito cewa, hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a samu yanayin zafi da rana amma za a samu ruwan sama da iska a wasu sassan Najeriya.

Kara karanta wannan
"Haka Allah ya tsara," 'Dan takarar APC, Jamilu Gwamna ya nemi hadin kan Pantami a Gombe
Wasu jihohin Arewa da Kudancin ƙasar za su fuskanci iska mai karfi da kuma ruwan sama mai yawa, tun daga safiya har zuwa yammacin ranar.
NiMet ta buƙaci matafiya da direbobi da su kasance masu taka-tsantsan yayin tuki domin guje wa haɗurran da rashin ganin nesa saboda iska mai karfi ke yawan haddasawa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

