Abin Tausayi: Tsohon 'Dan Majalisar Tarayya, Anas Adamu Ya Rasu a Hannun 'Yan Bindiga

Abin Tausayi: Tsohon 'Dan Majalisar Tarayya, Anas Adamu Ya Rasu a Hannun 'Yan Bindiga

  • Tsohon dan majalisar wakilan tarayya daga jihar Jigawa, Hon. Abba Anas Adamu, ya rasu a hannun masu garkuwa da mutane
  • Rahotanni sun nuna cewa an sace tsohon dan Majalisar ne tare da abokinsa Ali Tukur Gantsa a hanyar Kaduna zuwa babban birnin tarayya Abuja
  • Bayan biyan 'yan ta'addan kudin fansar da suka nema, sun sako Gantsa da rai yayin da aka gano gawar Hon. Adamu a cikin daji

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Jigawa, Nigeria - An tabbatar da rasuwar tsohon dan Majalisar wakilai daga jihar Jigawa, Hon. Abba Anas Adamu bayan ya fada hannun 'yan bindiga a hanyar Abuja.

Hon. Abba dai ya kasance tsohon shugaban kwamitin harkokin shari’a da ladabtarwa na majalisar wakilai kuma jigo a jam’iyyar hadaka, ADC a jihar Jigawa.

Abba.
Tsohon dan Majalisar wakilai daga jihar Jigawa, Abba Anas Adamu a wurin taron siyasa Hoto: Hon. Bashir Adamu
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta wallafa rahoto a yau Litinin, 10 ga watan Mayu, 2026, cewa Hon. Abba Anas Adamu, ya rasu yayin da yake hannun masu garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

Fada ya barke tsakanin kungiyoyin 'yan bindiga a Zamfara, an kashe hatsabibin jagora

Yadda aka sace tsohon dan Majalisa

An yi garkuwa da Hon. Abba Anas tare da abokinsa kuma abokin siyasa, Alhaji Ali Tukur Gantsa, a yankin Rijana da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja yayin da suke kan hanyar dawowa Kano.

Rahotanni sun ce masu garkuwar sun fara neman kudin fansa har Naira miliyan 200 daga iyalansa, kafin daga bisani suka sauko kuma amince a ba su Naira miliyan 50 bayan doguwar tattaunawa.

Shin an biya maharan kudin fansa?

Bayanan da suka fito da yammacin yau Litinin, sun nuna cewa bayan kai wadannan kudi, 'yan bindigar sun jefar da gawarsa, inda duka bukaci yan uwansa su je su dauka.

An tabbatar da mutuwar Hon. Adamu ne bayan masu garkuwar sun karbi kudin fansa sannan suka jagoranci dansa zuwa inda suka aje gawarsa.

Marigayin Abba shi ne tsohon 'dan majalisar tarayya wanda ya wakilci mazabar Guri/Kirikasamma/Birniwa ta jihar Jigawa.

A gefe guda kuma, an tabbatar da cewa Alhaji Ali Tukur Gantsa ya samu ‘yanci da ransa bayan an biya kudin fansa ga yan ta'addan, cewar rahoton Guardian.

Kara karanta wannan

Rikicin Yobe: mutum 6 da aka hana takarar gwamna a APC sun gana da Kashim Shettima

Majalisa.
Zauren Majalisar wakilai da ke babban birnin tarayya Abuja Hoto: @HouseNGR
Source: Twitter

An fara shirin jana'iza a jihar Kano

Yanzu haka dai majoyoyi sun tabbatar da cewa an dauko gawar tsohon Majalisar zuwa jihar Kano domin yi mata jana'iza kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Sai dai har kawo yanzu ba a bayyana lokacin da za a yi jana’izar marigayin ba, amma ana sa ran ba za a yi wani jinkri ba bayan gawar ta isa Kano.

Lamarin ya jefa iyalai, abokai, abokan siyasa da al’ummar jihar Jigawa cikin alhini da jimami yayin da mutane da dama ke ci gaba da mika sakon ta'aziyya.

Sarki ya mutu a hannun 'yan bindiga

A baya, kun ji cewa wani basarake a Oke-Ere da ke ƙaramar hukumar Yagba ta Yamma a jihar Kogi, Adebayo Samuel ya rasu a hannun masu garkuwa da mutane.

An sace Samuel ne ranar 21 ga Afirilun 2026 da misalin ƙarfe 10:00 na safe yayin da yake gudanar da ayyukan noma a wata gona da aka noma a yankin Odo-Ere.

Kokarin da aka rika yi da nufin ceto Sarkin ya kai karshe bayan rahotanni sun bayyana cewa Samuel ya rasu a hannun masu garkuwa da mutanen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262