Isra'ila Ta Hukunta Sojojin da Suka Ci Mutuncin Mutum Mutumin Mamar Yesu Almasihu

Isra'ila Ta Hukunta Sojojin da Suka Ci Mutuncin Mutum Mutumin Mamar Yesu Almasihu

  • A kwanakin baya sojojin Isra'ila sun janyo cece-kuce bayan wulakanta mutum mutumi na mamar Yesu Almasihu a Kudancin Lebanon
  • Bayan yaduwar hotunan wulakancin da sojojin suka yi, rundunar sojojin Isra'ila ta ve ta kaddamar ta bincike kan lamarin
  • Rundunar sojojin ta bayyana cewa ta yankewa sojojin da ke da hannu a aika-aikar zama a gidan yari sakamakon laifin da suka yi

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Tel-Aviv, Isra'ila - Rundunar sojojin Isra'ila ta bayyana cewa ta yanke wa wasu sojoji biyu hukuncin ɗauri a gidan kurkuku.

Rundunar sojojin ta Isra'ila ta yanke hukuncin ne bayan an ɗauki ɗaya daga cikinsu hoto yana sanya taba sigari a bakin mutum-mutumin mamar Yesu Almasihu a Kudancin Lebanon.

Sojan Isra'ila ya wulakanta mamar Yesu
Sojan Isra'ila na sanya taba sigari a bakin mutum mutumin mamar Yesu Almasihu Hoto: Midde East Mirror
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar sojojin Isra'ila ta sanya a shafinta na X a ranar Litinin, 11 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun yi wa 'yan ta'adda kwanton bauna a Katsina, an kashe tsageru

Sojan Israila ya wulakanta mutum mutumi

Wani hoto da aka yaɗa sosai a shafukan intanet ya nuna wani sojan Isra'ila rungume da mutum-mutumin mahaifiyar Yesu Almasihu yayin da yake danna taba sigari a bakinta.

A cewar rundunar sojojin, lamarin ya faru ne makonni da dama da suka gabata a Kudancin Lebanon, kuma kwamandojin da ke wurin sun gudanar da bincike akai.

An hukunta sojojin Isra'ila

"Bayan kammala bincike, an yanke wa sojan da aka gani yana aikata danyen aikin hukuncin kwanaki 21 a gidan yarin sojoji, sannan sojan da ya ɗauki hoton lamarin an yanke masa hukuncin kwanaki 14 a gidan yarin sojoji."

A wani sako daban da ta wallafa a shafin X, kakakin rundunar sojojin, Laftanar Kanar Ariella Mazor, ta bayyana cewa:

"Rundunar IDF tana kallon wannan lamari da matuƙar muhimmanci kuma tana jaddada cewa halayyar sojan ta kauce wa kyawawan dabi'un da ake sa ran sojojinta su nuna."

Wannan ba shi ne karon farko da rundunar sojojin Isra'ila ke fuskantar suka a makonnin baya-bayan nan game da halayyar sojojinta dangane da gumaka ko mutum-mutumi na addinin Kiristanci a Kudancin Lebanon ba.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojoji sun dakile mummunan harin yan ta'adda, sun tura 50 lahira a Yobe

An hukunta sojojin Isra'ila
Manyan sojojin Isra'ila a wajen taro Hoto: @IDFonline
Source: Twitter

Ana samun sojojin Isra'ila da laifi

A ƙarshen watan Afrilu, rundunar sojojin ta ce wasu sojoji biyu za su kwashe kwanaki 30 a gidan yarin sojoji sannan za a cire su daga aikin fagen fama sakamakon lalata mutum-mutumin Yesu Almasihu a ƙauyen Debl da ke kudancin Lebanon.

A wancan lamarin, an yaɗa wani hoto a intanet da ke nuna wani sojan Isra'ila yana amfani da babbar guduma yana dukan kan mutum-mutumin Yesu da aka gicciye.

"Rundunar IDF tana girmama ’yancin addini da na yin ibada, da kuma wurare masu tsarki da alamomin addini na dukkan addinai da al'ummomi."

- Ariella Mazor

Hezbollah ta kashe sojan Isra'ila

A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Hezbollah ta kai hare-hare ta hanyar amfani da jirage marasa matuka mau dauke bama-bamai kan sojojin Israila.

Mayakan na Hezbollah sun kashe sojan Isra’ila guda ɗaya, yayin da wani kuma ya ji rauni matsakaici a harin wanda aka kai a Kudancin Lebanon.

Sojan da aka kashe an bayyana sunansa da Sgt. Liem Ben Hamo, ɗan shekara 19, na bataliya ta 13 a rukunin Golani, wanda ya fito daga Herzliya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng