'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Hallaka Babban Soja a Wani Hari a Borno

'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Hallaka Babban Soja a Wani Hari a Borno

  • An sake shiga jimami a jihar Borno sakamakon wani sabon harin ta'addanci da ƴan ta'addan Boko Haram suka kai
  • Ƴan ta'addan ƙungiyar Boko Haram sun farmaki wani ƙauye dake ƙaramar hukumar Gwoza a daren ranar Laraba
  • Harin da ƴan ta'addan suka kai ya jawo asarar rayukan jami'an tsaro, yayin da dakarun sojoji suka kashe wasu daga cikin masu tayar da ƙayar bayan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Ƴan ta’addan Boko Haram sun kai sabon harin ta'addanci a jihar Borno.

Ƴan ta'addan Boko Haram sun kashe wani Kyaftin ɗin sojoji a harin da suka kai a ƙauyen Izge da ke ƙaramar hukumar Gwoza a jihar Borno.

'Yan Boko Haram sun kai hari a Borno
'Yan ta'addan Boko Haram sun kashe sojoji a Borno Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ƴan ta’addan sun kai harin ne a daren ranar Laraba da misalin karfe 1:00 na dare, inda suka kuma kashe wani soja guda ɗaya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan Boko Haram sun kai hari a Borno

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, Sarkin Gwoza, Mai Martaba Alhaji Mohammed Shehu Timta, ya ce maharan sun mamaye yankin ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare sannan suka fafata da dakarun sojoji.

“Gaskiya ne cewa mutanena na garin Izge sun fuskanci hari daga Boko Haram da misalin ƙarfe 1:00 na dare. Abin baƙin ciki, wani Kyaftin da soja ɗaya sun rasa rayukansu."
“Amma dakarunmu masu jarumta, CJTF, mafarauta, da ƴan sa-kai tare da goyon bayan mazauna yankin sun kashe ƴan ta’adda uku."
"Ƴan ta’addan sun bar makamansu, babura sama da guda 10, kuma har yanzu suna gudu yayin da jami’an tsaro suka bi bayansu."

- Alhaji Mohammed Shehu Timta

An yi wa sojojin Najeriya addu'a

Ya yi addu’a ga waɗanda suka rasa rayukansu, sannan ya yabawa dakarun da suka haɗa kai da sauran jami’an tsaro wajen daƙile harin, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

“Allah (SWT) Ya sanya su a Jannatul Firdaus. Jarumanmu har yanzu suna cikin daji suna sadaukar da rayukansu domin tabbatar da zaman lafiya a cikin al’umma."

- Alhaji Mohammed Shehu Timta

'Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari a Borno
'Yan Boko Haram sun kashe Kyaftin na soja a Borno Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Sarkin ya kuma godewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, bisa tallafin kayan aiki da ya bai wa jami’an tsaro, tare da kira ga gwamnatin tarayya da ta samar da kayan yaƙi na zamani ga jami’an tsaro.

A cikin ƴan kwanakin nan dai ƴan ta'addan Boko Haram sun zafafa kai hare-haren ta'addanci a jihar Borno.

Ɗan majalisa ya koka kan Boko Haram

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan majalisar wakilan Najeriya mai wakiltar Gwoza/Damboa/Chibok a jihar Borno, Ahmed Jaha, ya nuna damuwa kan ƙaruwar hare-haren Boko Haram.

Ɗan majalisar ya bayyana cewa ƴan ta'addan sun sauya salo inda yanzu suka koma amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai hare-hare.

Ahmed Jaha ya nuna cewa makaman da ƴan ta'addan suke amfani da su, sun kere na dakarun sojojin Najeriya nesa ba kusa ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng