An Kama Mai Cire Sassan Jikin Mutum a Makabarta domin Tsafin Yin Kudi

An Kama Mai Cire Sassan Jikin Mutum a Makabarta domin Tsafin Yin Kudi

  • Rundunar 'yan sanda ta jihar Lagos ta kama wani matashi dauke da sassan jikin mutum a cikin jakarsa a yankin Epe
  • Wanda ake zargin ya ce ya tono sassan ne daga kaburbura a Edo da kuma gawarwakin mutanen da suka rasu a hadura
  • Rundunar 'yan sandan Lagos ta ce an kama matashin ne yana kokarin kai sassan jikin ga boka domin yin tsafi don samun kudi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - Rundunar ‘yan sandan jihar Lagos ta kama wani matashi dan shekara 25 mai suna Samson Oghenebreme bisa zargin safarar sassan jikin dan Adam.

An kama shi ne a unguwar Epe lokacin da ya ke dauke da jakar da ke kunshe da sassan jiki da ake zargin na mutum ne.

Legas
An kama mai satar jikin mutum a makabarta. Hoto: Lagos State Police Command|Getty Image
Asali: Facebook

'Yan sanda sun kama shi da jikin mutane

'Yan sanda sun wallafa a X cewa an kama Samson ne bayan ya jawo hankalin su saboda yadda ya ke tafiya kamar yana cikin maye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa bayan an binciki jakarsa, sai aka gano sassan jikin da ake zargi ya fito da su daga Edo.

A cewar wata majiyar ‘yan sanda, Samson ya amsa cewa ya tono sassan ne daga kaburburan da aka birne sababbin gawa a jihar Edo.

Har ila yau, ya kara da cewa yana kwaso sassan daga gawarwakin mutanen da suka mutu a hadura da aka bar su a gefen hanya.

Samson na kokarin mika sassan mutum ga boka

Wani jami’in ‘yan sanda ya ce duk da cewa Samson ya ce yana safarar sassan ne daga Edo, akwai alamun cewa manufarsa ita ce yin amfani da su wajen tsafin kudi.

Majiyar 'yan sanda ta ce:

“Daga dukkan alamu, Samson yana cikin wani gungun matasa da ke fama da cutar son saurin yin kudi, wadanda ke neman arziki cikin gaggawa ta hanyar amfani da sihiri,”

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Lagos, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da cafke Samson a ranar 25 ga Afrilu, 2025.

An mika mai satar sassan jikin mutum Edo

A cewar Hundeyin, binciken farko ya nuna cewa Samson yana kokarin kai sassan jikin ne zuwa ga wani boka domin yin asiri na neman arziki.

Kakakin 'yan sandan ya ce sassan da aka kwato an mika su zuwa babban asibitin Epe domin adanawa.

Hundeyin ya ce:

“An mika shari’ar ga rundunar ‘yan sandan jihar Edo domin ci gaba da bincike da gurfanar da wanda ake zargin a kotu,”
Yan sanda
Yan sanda sun bukaci hadin kan al'umma wajen yaki da laifuffuka. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Rundunar ‘yan sandan ta yi kira ga jama’a da su ci gaba da kai rahoto game da duk wani motsi da suke zargin yana da alaka da laifuffuka, musamman masu nasaba da sihiri

Matashi ya kashe mahaifinsa a Jigawa

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Jigawa ta kama wani matashi da ake zargi da kashe mahaifinsa da adda.

Ana zargin matashin ya yi amfani da adda wajen sassara mahaifinsa wanda ya yi sanadiyyar mutuwar shi.

Kakakin 'yan sandan jihar ya bayyana cewa an kama matashin ne a garin Sara da ake karamar hukumar Gwaram ta jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng