'Yan Sanda Sun Yi Magana kan Kasuwar Sayar da Sassan Jikin Dan Adam

'Yan Sanda Sun Yi Magana kan Kasuwar Sayar da Sassan Jikin Dan Adam

  • Rahotanni na nuni da cewa rundunar ‘yan sandan Filato ta yi bayani kan yiwuwar samuwar wata kasuwa da ake sayar da sassan jikin mutum a jihar
  • Kakakin ‘yan sandan jihar ya tabbatar da cewa kisan gilla da ake domin yin tsafe-tsafe da zai sanya samun irin kasuwar ya yi matukar kadan a Filato
  • Wani malamin addinin Kirista, Fasto Polycarp Lubo ya bukaci iyaye su hana ‘ya’yansu shiga kungiyoyin asiri da damfara domin samar da zaman lafiya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Filato - Rundunar ‘yan sandan Jihar Filato ta ce babu wani rahoto da ke nuna cewa ana sayar da sassan jikin mutum a jihar.

'Yan sandan sun yi bayani ne bayan samun jita jita kan samuwar irin kasuwar a jihar da mutane ke yawan yi.

Kara karanta wannan

Masu garkuwa sun yi amfani da jirgin sama wajen satar mutum a Kano

Yan sanda n Najeriya
'Yan sanda sun karyata labarin kasuwar sayar da sassan jikin mutum a Filato. Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Kakakin rundunar, Alfred Alabo ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a garin Jos.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, babu wata shaida ko rahoton sirri da ke nuna cewa akwai masu cin naman mutane ko kasuwar sayar da sassan jikin mutum a Filato.

Maganar tsafe tsafe a jihar Filato

Alfred Alabo ya yi magana kan tsafe tsafe bayan jaddada cewa ba a samu rahoton wata kasuwar sassan jikin mutum a jihar ba.

Kakakin 'yan sandan ya ce:

“Babu wani rahoton sirri da ke nuna cewa ana sayar da sassan jikin mutum a Filato; irin wannan ba ya faruwa a nan.
"Kuma zan iya tabbatar da cewa kisan gilla na tsafe-tsafe yana da matukar kadan a jihar.”

Maganar 'yan sanda kan damfara

Sai dai kakakin ‘yan sandan ya ce ana samun masu damfarar mutane ta kafafen sada zumunta, da ake kira ‘Yahoo Boys’, da ke amfani da hanyoyin tsafi.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bude wuta kan masu taron siyasa a Najeriya, an harbi mutane 14

Alfred Alabo ya ce:

“Yawancin su suna kashe mutane tare da fitar da sassan jikinsu don yin tsafi, a bisa umarnin bokaye da ke ba su shawarar yadda za su samu nasara da kuma kauce wa kamawa.”

Haka zalika, ya ce matsalar satar mutane, fashi da makami da kuma ayyukan kungiyoyin asiri na karuwa a wasu yankunan jihar.

Fasto ya bukaci iyaye su tsawatarwa 'ya'ya

A nasa bangaren, Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) a Filato, Rabaran Polycarp Lubo, ya bukaci iyaye su hana ‘ya’yansu shiga kungiyoyin asiri.

Punch ta wallafa cewa Rabaran Polycarp Lubo ya bukaci iyaye su ja kunnen 'ya'yansu kan shiga harkar damfarar mutane ta kafafen sada zumunta.

Faston ya ce ya dace malamai da shugabannin addini su rika wayar da kan jama’a kan hatsarin tsafi da kisan gilla domin hana yaduwar wadannan laifuffuka a cikin jama'a.

Gwamnan Filato
Gwamnan Filato, Caleb Mutfwang. Hoto: Plateau Sate Government
Asali: Twitter

An rusa gidan masu garkuwa a Edo

Kara karanta wannan

Yadda sufetan 'dan sanda da matasa suka lakadawa tsinannen duka ya rasu a Jos

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Edo ta fara daukar matakin rusa gidajen masu garkuwa da mutane da aka gano suna boye wadanda suka sace.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin jihar ta gargadi masu ba da hayar gidaje da su guji mika gidajensu da wadanda ba su san halinsu ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng