Oyo: An Tsinta Gawar Mutum 3, An Cire Wasu Sassan Jikinsu

Oyo: An Tsinta Gawar Mutum 3, An Cire Wasu Sassan Jikinsu

  • Wasu matasa uku sun ziyarci barzahu, yayin da wasu wadanda ba a san ko su waye bane suka aika su lahira a Ibadan, babban birnin jihar Oyo
  • An ruwaito yadda wadanda ake zargin matsafa ne suka yanki sassan jikin biyu gami da cire kan daya a safiyar Litinin a karamar hukumar Akinyele
  • Wani direba ya labarta yadda ya ga gawawwakinsu da safiyar Litinin yayin da ya dauko fasinjoji daga Ojoo zuwa Toose

Oyo - An ruwaito yadda matasa uku suka rasa rayukansu a safiyar Litinin bayan wasu wadanda ba a san ko su waye ba sun kai musu farmaki a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Lamarin ya auku ne wuraren tashar motar Ofis, bayan gidan man World Oil a sabon titin Ibadan a karamar hukumar Akinyele na jihar.

Kara karanta wannan

"Abin Da Ya Janyo Rasuwar Ƴaƴa Na 2", Buhari Ya Yi Magana Kan Wani Sirrinsa Mai Sosa Zuciya

Taswirar Oyo
Oyo: An Tsinta Gawar Mutum 3, An Cire Wasu Sassan Jikinsu. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Jaridar Punch ta rahoto cewa, binciken da manema labarai suka yi ya bayyana yadda lamarin ya auku da safiyar Litinin.

Haka zalika, an tattaro yadda suka cire kan daya daga cikin wadanda lamarin ya auku dasu yayin da aka yanki sassan jikin sauran biyun.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wani 'dan tasi, Abdfatai AbdulGaniyu ya ce:

"Naga gawawwakinsu da safiyar yau, yayin da na dauko fasinjoji daga Ojoo zuwa Toose yau. Wannan lamarin yayi kama da tsafi saboda an cire kan daya daga cikinsu."

Wata majiya wacce ta bukaci a sakaya sunanta ta ce:

"Fasinjojin na neman sauki, motocin haya masu sauki sun saba tsayawa a tashar motar don daukarsu zuwa Oyo, Ogbomoso, Illorin da Jebba.
"Ba sa iya biyan kudin motar a babbar tasha, shiyasa suka tsaya nan. Amma wannan lamarin daban ne saboda an yanki wasu mahimman sassan jikinsu."

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Wani Kazamin Hari Jihar Arewa, Sun Kashe Basarake

Zuwa lokacin tattara wannan rahoton, duk iya kokarin da aka yi don zantawa da kakakin 'yan sandan jihar, Adewale Osifeso bai yuwu ba, saboda lambar wayarsa ba ta shiga.

Bayelsa: Saniya Kirsiemti ta Tumurmusa shugaban matasa

A wani labari na daban, wata saniyar Kirsimeti a garin Yenagoa ta halaka shugaban matasa bayan wadanda suka je yankata basu daure ta da kyau ba.

Ta tashi tare da yin ciki da shi inda ta dinga buga shi da kasa har da lokacin da aka ccece shi.

Sai dai bayan an kai shi asibiti, yace ga garin ku sakamakon miyagun raunikan da ya samu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel